Rashin aikin yi tsakanin matasa a Nijeriya ya kai kololuwa. Rahoton ya kiyasta cewa kusan matasa miliyan 80 a Nijeriya ba su da aiki a halin yanzu, wanda ke wakiltar kusan kashi 53 cikin dari na yawan matasan qasar, abin da ke nuna girman matsalar rashin aikin yi a tsakanin mutane masu shekaru kimanin 15 zuwa 35 a faɗin kasar.
Nijeriya na fitar da kusan ɗalibai masu digiri 600,000 duk shekara daga jami’o’i da kwalejoji. Kowace shekara, kusan matasa miliyan 1.8 na Nijeriya na shiga neman aiki, amma kusan ayyuka 450,000 ne kaɗai hukuma ke iya samarwa duk da tattalin arzikin kasar.
- An Bukaci Amurka Da Ta Kauracewa Sanya Wasu Sassa Na Muzgunawa Kasar Sin Cikin Kudurin Dokar Tsaron Kasa
- GORON JUMA’A
Lissafin yana da tsauri, inda ɗalibai da yawa ke neman ayyuka kaɗan, kuma ribar samun ilimi mai zurfi na raguwa. Idan ka samu ɗalibai biyar guda xaya ne a cikinsu ke samun aiki wanda ba ya bukatar digiri mai albashin da ba ya ɗorewa.
A Abuja, Ifeanyi Nwokedi, matashi ne xan shekara 26 mai digiri a Fannin Harkokin Yaɗa Labarai, cewa ya yi ya nemi aiki fiye da 150 tun bayan kammala hidimarsa ta NYSC a 2023.
“Kowace safiya na kan tashi in duba allunan tallan aiki. Ina zuwa ganawa da ma’aikata, ina yin horon aiki ba tare da albashi ba, amma babu abin da ke kai wa ga samun aiki. Masu daukar ma’aikata suna cewa suna rage ma’aikata ko dakatar da daukar ma’aikata. Kamar tsarin da ake cewa ba mu gurbin aiki,” ya shaida wa NATIONAL ECONOMY.
Da yawa daga cikin matasan da ke aiki wadanda a da suke samun mafaka a harkokin kanana na kasuwanci sun ce ko wadannan hanyoyin sun rushe saboda hauhawar farashin kayayyaki da ta sanya kudin gudanarwa ya zarce abin da za a iya biya.
A Legas, Bilikisu Abdullah, mai gyaran gashi da kananan kasuwanci, ta ce ta rufe karamin shagonta na gyaran gashi a watan Agusta bayan kudin haya ya ninka sau biyu kuma farashin kayan gyaran gashi ya ninka sau uku. “Ban so na kori yarinta ba, amma babu abin da zan iya yi,” in ji ta.
“Yanzu mu duka muna gida. Ina aika CB kowace rana, amma ban sami amsa ba,” in ji ta.
Sashen masana’antu, wanda a al’ada ke daya daga cikin manyan masu ba da aikin yi a Nijeriya, na ci gaba da rasa ayyuka yayin da masu masana’antu ke fama da rashin tabbas na canjin kimar musayar kudi, farashin dizal, da cikas wajen shigo da kayayyaki.
Kungiyar Masu Kera Kayayyaki ta Nijeriya (MAN) kwanan nan ta yi gargadin cewa daruruwan kamfanoni na aiki kasa da kashi 40 cikin dari na karfinsu.
Wani jami’in alakar masana’antu a Jihar Ogun, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce akalla masana’antu12 masu matsakaicin girma a yankin Agbara sun sallami ma’aikata tsakanin watan Yuni zuwa Oktoba.
“Muna cikin koma-baya na aikin yi,” in ji dan tattalin arziki mai zaune a Legas, Akin Adesina. “Tattalin arzikin na girma a hankali sosai don daukar miliyan biyu na matasa da ke shiga kasuwar aiki kowace shekara.”
“Idan ka hada karancin zuba jari, rashin tabbas na musayar kudi, karancin samar da kayayyaki a masana’antu, da hauhawar farashin rayuwa, sakamakon shi ne rashin aikin yi mai yawa.”
Matsalar ta kara tsananta rashin tsaro. Masana tsaro sun ce matasan da ba su da aiki suna kara zama abin da kungiyoyin laifi, hanyoyin rarraba miyagun kwayoyi, da kungiyoyin masu makami ke nema a duk yankunan arewa da kudu.
Hukumar ‘yansanda a Jihar Filato da Kaduna kwanan nan ta danganta karuwa a laifukan da suka shafi matasa da kalubalen tattalin arziki da ake fuskanta.
Hukumar gwamnati na jaddada cewa gyare-gyaren zai dauki lokaci kafin ya haifar da sakamako. Wani babban jami’i a Ma’aikatar Kwadago da Ayyukan Yi, wanda ya yi magana kan sharadin a sakaya sunansa, ya ce gyare-gyaren tattalin arziki da ake gudanarwa zai kara samar da ayyuka idan tattalin arzikin kasa ya samu daidaito.
“Mun fahimci takaicin, amma manufofin da aka kafa suna nufin jawo zuba jari, daidaita kudin kasa, da tallafa wa masana’antu,” in ji shi.
Sai dai masu sukar gwamnati sun ce dabarun ba na gaggawa bane. Masu fafutukar matasa sun ce martanin manufofi ya yi jinkiri sosai kuma ba shi da fadi don magance girman matsalar.
“Ba za mu iya jiran shekaru uku har a cimma wadannan gyare-gyare ba, yayin da miliyoyi ke fadawa cikin talauci. Nijeriya na bukatar shirin gaggawa na samar da ayyuka ga taron jama’a, tallafi na musamman ga kananan kasuwanci, da gyara horon sana’o’i.
Matasa ba kawai kididdiga ba ne; su ‘yan kasa ne masu burin rayuwa,” in ji masanin tattalin arziki a fannin kwadago a ‘Nigerian Economic Summit Group, Dr. Musa Yusuf.
Masana sun yarda cewa hanyar da za ka samu aiki da zarar ka samu ilimi ta lalace.
Jami’o’i na fitar da dalibai a fannonin da kasuwa ba ta da bukata sosai. Masu daukar ma’aikata suna korafin rashin kwarewa. A gefe guda, cibiyoyin horo na sana’o’i da fasaha, wadanda suka yi matukar muhimmanci wajen kara damar samun aiki, suna fama da karancin kudi.
A Legas, Mofe Adetokunbo, dan shekara 23 mai digiri a Injiniyan Injina, ya bayyana wannan takaici. “Na yi karatun da ya shafi aiki a aikace, amma kusan ba mu taba amfani da injuna a makaranta ba. Yanzu kamfanoni suna bukatar kwarewa.
Ta yaya mutumin da bai taba ganin injin lathe a makaranta ba zai samu kwarewa?” in ji shi.
Sakamakon rashin daukar mataki na iya zama mai muni. A cewar masanin tattalin arziki a fannin ci gaban kasa, Dr. Ifeanyi Okeke, Nijeriya na fuskantar wani muhimmin lokacin canji.














