Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Sun Lei, ya ce ya zama wajibi tawagar MDD mai aikin wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo wato MONUSCO a takaice, ta wanzar da cin gashin kai yayin da take gudanar da ayyukanta.
Sun Lei, wanda ya bayyana hakan a jiya Jumma’a, ya kara da cewa tawagar MONUSCO na karshin jagorancin MDD, tana kuma aiwatar da ayyukan da kwamitin tsaron majalisar ya dora mata, kuma Sin na goyon bayanta a fannin taka rawar gani, wajen ingiza shirin zaman lafiya a gabashin Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo. Ya ce ba wata kasa da ya kamata, bisa son rai, ta karkata ayyukan MONUSCO daidai da ajandarta ta siyasa.
Yayin da yake karin haske, bayan majalisar da babban rinjaye ta zartar da kuduri mai lamba 2,808, na sabunta wa’adin aikin tawagar ta MONUSCO da karin shekara guda, ya ce wajibi ne kwamitin tsaron MDD ya rungumi matsayin cin gashin kai, da rashin nuna bambanci, da kare ikon tawagar MONUSCO, kana ya nacewa muhimman ka’idojin jagorancin ayyukan wanzar da zaman lafiya. Domin ta haka ne kadai MONUSCO za ta samu amincewa, da goyon bayan daukacin membobin MDD. (Saminu Alhassan)














