Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sauya sunan Jami’ar Kimiyyar Lafiya mallakin Gwamnatin Tarayya da ke Azare zuwa sunan Sheikh Dahiru Usman Bauchi domin tunawa da marigayin.
Tinubu ya misalta marigayin a matsayin babban malamin da ya hidimta wa addinin Musulunci wanda ya yi aiki domin Allah.
- Ban Dogara Da Harkar Fim Shi Kadai A Rayuwata Ba — Maryam Usman(2)
- An Fara Aiki Da Na’urar Fasahar Samar Da Lantarki Daga Iskar CO₂ Da Aka Sarrafa A Lardin Guizhou Na Kasar Sin
Shugaban ƙasar ya tabbatar da cewa Sheikh Dahiru ya yi tasiri sosai wajen inganta harkokin ilimin al’ummar Bauchi da ma Nijeriya baki ɗaya.
Hakazalika, ya ce, magayin ya rungumi ɗa’a ta ƙwarai wanda ya yi amfani da rayuwarsa cikin dattako da kamala.
Shugaban wanda ya ziyarci Jihar Bauchi a ranar Asabar, domin jajanta wa iyalan marigayin bisa rashin da suka yi, ya misalta rasuwar a matsayin babban rashi ga kasa baki ɗaya.
Tinubu, ya ƙara da cewa Sheikh Dahiru ya kasance mutum mai ƙima wanda ya sanya kishi da son Nijeriya a zuciyarsa.
Shugaban ƙasar ya yi amfani da damar wajen kira ga al’umma da su ci gaba da yi wa ƙasar nan addu’ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali, tare da bunƙasar tattalin arziƙi, ci gaba da rayuwa mai inganci.
Ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan malamin, ya kuma sanya shi a Aljanna maɗaukakiya.
Gwamnan Jihar Bauchi Bala Muhammad, ya nuna farin cikinsa da karamcin da shugaban ƙasar ya yi wa iyalan .amacin da kuma al’umman jihar, tun daga lokacin rasuwar malamin har zuwa yau da ya zo jihar da kansa domin jajantawa duk da tawagogin da ya yi ta turowa.
Da yake magana a madadin iyalan marigayin, Khalifansa Sheikh Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya ce tabbas ba za su taɓa mantawa da mutuntawa da karamcin da shugaban ƙasa ya musu ba.
Dakta Bashir Sheikh Dahiru Usman Bauchi, shi ne ya miƙa saƙon a madadin Khalifan, ya ce tun ranar jana’izar mahaifinsu Tinubu ya turo tawaga ta musamman ƙarƙashin mataimakinsa, Kashim Shettima domin halartar jana’izar daga baya kuma ya sake turo tawaga domin yi musu ta’aziyya.
“Yau kuma ga shi da kansa ka zo domin jajanta mana gaskiya mun gode da wannan karamci.”
“A madadin dukkanin iyalan Sheikh Dahiru Usman Bauchi, mabiya da magoya bayansa, tabbas muna miƙa godiya ta musamman ga shugaban ƙasa bisa karamcin da ya yi mana.”





























