Gwamna Uba Sani ya sake nanata alƙawarinsa na gina ƙasa inda bambancin ra’ayi zai zama shine tushen ƙarfinmu kuma kowane ɗan ƙasa zai iya rayuwa cikin mutunci da salama.
Gwamnan, wanda ya bayyana hakan a yayin da ya kasance mai masaukin baƙi a wurin taron bikin cika shekaru 50 da kafuwar Ƙungiyar Agajin Musulunci ta Nijeriya, Jama’atu Nasril Islam (JNI) a ranar Asabar, ya ce, hangen nesan ƙungiyar ya dogara ne akan haɗin kai, zaman lafiya, da samar da ci gaba mai ɗorewa.
- Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN
- Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Ya kuma ce, wannan hangen nesan ne ke jagorantar gwamnatinsa wajen fifita tsaro, dawo da ƙwarin gwiwa, da ba da damar ‘yancin walwala a tsakanin al’ummomi da suka taɓa kasancewa cikin tsoro da firgici.
Gwamna Uba Sani ya yaba da hangen nesa na waɗanda suka kafa Ƙungiyar Agajin, musamman marigayi Sarkin Sokoto, Sir Abubakar na III; marigayi Sarkin Katsina, Sir Usman Nagogo; marigayi Sheikh Abubakar Gummi; da Shattiman Katsina, Alhaji Muhammadu Ali Kaita.
A cewarsa, ”sun fahimta, a bayyane, cewa ƙarfin imani ba wai kawai ana auna shi ne ta hanyar ibada ba, har ma da hidimtawa ɗan adam.”
Ya gode wa shugabannin ƙungiyar JNI bisa karrama shi da suka yi na bashi muƙamin mai masaukin baƙi kuma ta ba shi kyautar girmamawa ta ƙwarewa a aiki.
Da yake jawabi a wurin taron, Sakatare Janar na JNI, Farfesa Khalid Abubakar Aliyu, ya gode wa Gwamna Uba Sani saboda ɗaukar nauyin taron.













