Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki zagon Kasa (EFCC), sun kama wasu mutane 19 da ake zargi da damfarar yanar gizo a wani samame da suka kai a Lokoja, jihar Kogi.
Jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa sun kama wadanda ake zargin ne a karshen mako.
Wadanda ake zargin sun hada da wani dan bautar kasa a jihar, Adamu Shuabu, da wasu 18.
Sauran sun hada da Achimugu Ojonoka, Victor Atsumbe, Akoh Grace, Usman Abubakar, Jacob Emmanuel, Solomon John, Christian Oyakhilome, Adesanya Adeolu, Uloko Ojonugwa da Timothy Moses, Negedu Onuchei, Usman Tenimu, Lukman Musa, Samuel Atadoga, Daniel James, Abdulrazaq Ahnod, Olarewaju Olumide da Ademola Daniel.
Bayan kama su, an kwato wata mota kirar Lexus, makudan kudade da ake zargin sun samu ne ta haramtacciyar hanya, nau’ikan wayoyi daban-daban, kwamfutoci da sauran kayayyaki Daban-daban.
Sanarwar da hukumar ta EFCC ta fitar ta ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kuliya da zarar an kammala bincike.