• English
  • Business News
Thursday, October 30, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Labarin Asadulmuluuk (39)

by Rabi'u Ali Indabawa
3 years ago
Labarin Asadulmuluuk (39)

“Assalamu alaikum.” suka amsa baki dayansu, “Wa’alaikussalama,” kansa a sunkuye bai kalle su ba, sannan ya ce; “Ina farin cikin haduwarmu a wannan majalisi mai albarka, Allah ya sa haduwar mu ta zama alkhairi a garemu baki daya, kuma ina kara taya mu murnar ganin shekarar budi da zaman lafiya.” 

Shahid bai san Hafida ba, kuma yana son ya fitar da ita a cikin kawayenta.

  • Cinikin Waje Na Kasar Sin Shi Ne Jigon Tattalin Arzikin Duniya
  • Xi Jinping Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Zababben Shugaban Kenya

Sai ya ce; “Ina rokon sakin fuska daga mai masaukin baki,” sai ya ga duk sun kalle ta sun yi murmushi, ita kuma ta jawo mayafin kanta ta rufe fuskarta saboda kunya.

Da ya fahimci haka ya girgiza kai, cikin zuciya ya fada, “Kai tsarki ya tabbata ga Ubangijin da ya kyautata halittu, lallai su Hafida da kawayenta ana zuba kyau a doron kasa.”

Shahidah ta kalli Hafida ta ce; “Hafida bakonki fa zuciyarsa cike take da sake-sake.”

LABARAI MASU NASABA

Gwarzon Mawaƙin Shekarar 2025, Skales

Neman Kudi Ne Ya Kawo Ni Masana’antar Kannywood Ba Fadakarwa Ba – Khadija Muhammad 

Nan ma ya dago kai ita ma ya kalle ta, sai ya rasa to wace mace za’a samu a wannan kasa da za ta haura wadannan ‘yan mata kyau? Kai lallai su Hafida ana zuba kyau.

Babu shakka abokina ba a banza ya haukace cikin kaunarta ba.

Bayan sun yi masa barka da zuwa, sai doki ya yi haniniya ta uku, wadda kuma ita ce ta karshe, a nan sai ya ce; “Ina neman afuwa zan je na isar da wani sako na dawo,” Hafida ta ce; “Sako kuma? Amma na ga doki fa yayi haninya, a wurin dokin kuma za ka karbi sakon? Ya yi murmushi ya mike tsaye ya fita.

Hafida ta kalli kawayenta ta ce, “In ce ko kun ga irin halayyar samarin, kuna ganin yadda yake ta fito da wasu al’amura ko? Amma ku ta shi mu bishi mu ga abinda zai aikata.”

Suka biyo shi a baya bai sani ba, da zuwansa suka ga yana magana da dokinsa da wani yare da ba su sani ba.

Da Hafida ta ga haka, nan da na ta koma cikin gida ta debo karti mutum shida wai su lura da zaman da za su yi da wannan bako, idan sun ji daya daga cikinsu ta yi kara su kawo musu dauki, don a tunaninta Shahid ba mai cikakken hankalin ba ne, ya juya zai koma cikin gidan, sai Layusa take gaya masa halin da ake ciki.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji
Manyan Labarai

Gwarzon Mawaƙin Shekarar 2025, Skales

October 25, 2025
Neman Kudi Ne Ya Kawo Ni Masana’antar Kannywood Ba Fadakarwa Ba – Khadija Muhammad 
Nishadi

Neman Kudi Ne Ya Kawo Ni Masana’antar Kannywood Ba Fadakarwa Ba – Khadija Muhammad 

October 11, 2025
Me Ya Sa Jaruman Masana’antar Kannywood Ke Auren Sirri?
Nishadi

Me Ya Sa Jaruman Masana’antar Kannywood Ke Auren Sirri?

October 11, 2025
Next Post
Auren Da Nake Buri

Auren Da Nake Buri

LABARAI MASU NASABA

Labarin Asadulmuluuk (39)

Bai Kamata Gwamnati Ta Ke Ciyo Bashi Bayan Cire Tallafin Man Fetur Ba – Sanusi II

October 30, 2025
Tinubu Ya Gaza Wajen Magance Matsalar Tsaro A Nijeriya — Atiku

Atiku Ya Soki Gwamnatin Tinubu Kan Sauya Sunayen Waɗanda Aka Yi Wa Afuwa

October 30, 2025
Sakamakon Nazarin CGTN Ya Yabawa Gudunmuwar Sin Ga Dunkulewar Yankin Asiya Da Pasifik

Sakamakon Nazarin CGTN Ya Yabawa Gudunmuwar Sin Ga Dunkulewar Yankin Asiya Da Pasifik

October 29, 2025
Asuu

Gwamnatin Tarayya Ta Saki Naira Biliyan 2.3 Ga ASUU

October 29, 2025
Sabon Ingantaccen Hadin Gwiwar “Sin-ASEAN 3.0″ Ya Kafa Sabon Misali Na Hadin Kan Yanki

Sabon Ingantaccen Hadin Gwiwar “Sin-ASEAN 3.0″ Ya Kafa Sabon Misali Na Hadin Kan Yanki

October 29, 2025
Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro

Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro

October 29, 2025
An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest

An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest

October 29, 2025
majalisar kasa

Majalisar Wakilai Ta Amince Da Bukatar Amso Bashin Dala Biliyan 2.34 A Kasuwar Jari Ta Duniya

October 29, 2025
An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin

An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin

October 29, 2025
Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC

Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC

October 29, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.