Fitacciyar Jarumar da ke haskawa a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood musamman cikin shiri mai dogon zango na Lu’u Lu’u, da IZZAR SO, Jarumar da aka fi sani da suna KHADIJA a cikin shirin Lu’u Lu’u wato HAUWA YUSUF MUHD, Ta bayyanawa masu karatu yadda farkon fara fim din ta ya kasance, tare da dalilinta na shiga harkar fim, gami da cewa, duk wacce za ta shiga harkar fim ta kasance da sanin iyayenta. Jarumar ta kuma yi kira ga Gwamnati dangane da ci gaban masana’antar Kannywood, har ma da wasu batutuwan da suka shafi rayuwarta ga dai tattaunawar tare da wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA Kamar haka:
Masu karatu za su so sanin cikakken sunanki tare da dan takaitaccen tarihinki.
Sunana Hauwa’u Yusuf Moh’d wacce aka fi sani da Khadija a cikin shirin LU’U LU’U. An haife ni a cikin garin Katsina a unguwar ‘Rafin Dadi’ dake cikin garin Katsina, a 1999 na kammala karatuna a 2017, Alhamdulillah ina da Izu 45 a makaratar Islamiya.
Ma sha Allah. To me ya ja hankalinki har kika tsunduma cikin harkar fim?
Abin da ya ja hankalina na shiga harkar fim saboda ina so in fadakar, kuma in tunatar wal’ummar Musulmi na duniya baki daya, hakan kuma ta samu nasaba da tun ina yarinya nake son masana’antar shirya fina-finai wacce aka fi sani da Kannywood.
Za ki yi kamar shekara nawa cikin masana’antar Kannywood?
Zan iya kai kamar kimanin shekara hudu 4 a masana’antar.
Nawa ne adadin fina-finan da kika yi?
Na yi fim mai suna Mubarek da Salmanu da Sai Mai Mota, Dan Chacha, Kansilan Kauye, da dai sauransu ba zan iya tuna adadinsu ba don na manta wasu, sai kuma wanda muke cikinsa a yanzu LU’U LU’U da IZZAR SO da HADARIN SO da SILAR SO duka ‘mai dogon zango’ ne.
A wanne fim kika fara fitowa, da wanne kika fara?
Na fara da Mubarek da Salmanu duk lokaci daya ne na fara da su.
Ya farkon farawarki ya kasance kasancewar shi ne farko a lokacin?
Gaskiya ko da na fara mutane da dama sun yi mamaki musamman da aka ce musu farkon farawa ne, sakamakon akwai abin a raina, kuma ina so shi ya sa ban ji wani dar a jikina ba.
Ko akwai abin da ya baki wuya a lokacin da za ki fara?
Gaskiya ban ji wuyar komai ba, sai dai jiki d a jini wanda baka saba da shi ba. Gaskiya ban sa komai a raina ba, komai aka ce na yi zan iya yi shi in sha Allah.
Toh ya gwagwarmayar shiga masana’antar ta kasance?
Cikin sauki ba tare da wata wahala ba, sakamakon ina da yaya ko in ce yayye a cikin masana’antar.
To batun iyaye kuma fa, Lokacin da kika sanar musu cewa kina sha’awar shiga harkar fim, ko akwai wani kalubale da kika samu daga gare su?
 Gaskiya ban samu ba, sai ma goyen baya da suka bani, sai dai a ce ko cikin ‘yan uwa a samu abin da ba a rasa ba.
A gaba daya fina-finan da kika yi idan aka ce ki fadi bakandamiyarki wanne za ki ce?
Zan iya cewa LU’U LU’U, saboda yanzu da shi ne aka fi sanina kuma aka fi kallon sa bisa ga na baya da suka wuce.
Wace rawa kika taka a cikin shirin Ku’u Lu’u?
Ni ce nake jan fim din ko kuma in ce miki ni ce ‘star’ a fim din labarin a kaina yake zan iya ce miki a takaice.
Lokacin da za a fara shirin Lu’u lu’u ke ce kika zabi fitowa a matsayin tauraruwar shirin ko kuwa wadanda suka shirya shirin ne suka ga kin dace da matsayin fitowa Tauraruwa?
A a! ba ni na zaba ba, sun tara masu ba da umarni da yawa da kuma masu daukar nauyin shiri suka ga na cancanci a sani matsayin tauraruwar shirin, da kuma zabin Allah.
Wanne irin farin ciki kika yi lokacin da kika ji cewa ke ce za ki zamo babbar tauraruwa a shirin?
Gaskiya na ji dadi sosai duk da ba shi kadai bane fim din da na ja sai dai a ce shi wannan me dogon zango ne ya sha bamban da na kasuwa da kuma gidajen TB kuma ina alfarahari da shirin fim din LU’U LU’U a ko da wane lokaci.
Na ji kin ce kin fito a shirin Izzar so, shi wacce rawa kika taka cikin shirin?
A cikin shirin fim din izzar so na taka rawa matsayin kanwar wanda ya tsinci Umar Hashim ne wato Alawiyya.
Ko akwai wani kalubale da kika taba fuskanta game da wannan sana’ar taki ta fim?
Ai faruwar kalubale nasara ce, kuma ba a fadarsa sai dai a bashi baya duk abin da ya wuce ya riga da ya wuce sai dai mu tunkari gaba.
To ya batun nasarori fa wanne irin nasarori kika samu game da fim?
Nasarori ma sai dai mu ce Alhamdulilahi Allah Ya kara wa Annabi daraja (S.A.W)
Me kike son cimma game da fim?
Ina so na kai matakin da kowa ya kai idan Allah ya amince, saboda komai da yardar mahalicci yake zuwa.
Ya kika dauki fim a wajenki?
Sana’a da kuma kaunar masana’antar idan na ce sha’awa na lokaci kalilan ne.
Wace ce babbar kawarki a Kannywood?
Kowa kawata ce.
Da wa kika fi so a hadaki a fim?
Da kowa ina jin dadin aiki, amma ina so a hada ni da Salisu S. Fulani.
Kar fa ki sa mutane su ce ko dai soyayyar ta gaske ce?
A a ko daya ba soyayya, sai dai ta Yaya da kanwarsa, amma ba ta gaske ba ce.
Ko kina da iyayen gida a kannywood?
Eh, Ina da su, akwai; Isah Bawa Doro, Balarabe Kabeer, Lawal Agga Sama’il Abba.
To, ya batun soyayya fa, ko akwai wani da ya taba kwanta miki a rai cikin masana’antar da har ta kai da kin fara soyayya da shi?
Babu ko daya ina da wanda nake so ni ma a gefe. Yaushe za ki aure?
Lokacin da Allah ya amince.
Wanne irin namiji kike son aura?
Ina son namiji mai tsoron Allah, mai addini, masanin Alkur’ani da Hadissan Manzon Allah mai kiyaye hakkin addinin Muslunci.
Bayan fim kina wata sana’ar ne?
Eh ina sana’ar kwalliya.
Akwai wani waje da kika bude wanda ki ke kwalliyar, ko kuwa a gida kike yi?
A gida nake yi, ina da burin budewa in Sha Allahu a nan gaba.
Ya kike iya hada sana’arki ta fim da ta kwalliya?
Lafiya kalau kuwa ai ba kullum ake fita aikin fim ba, haka ita ma kwalliyar, kuma ba su taba hade mun ba.
Wanne abu ne ya taba faruwa da ke na farin ciki ko akasin haka wanda ba za ki taba iya mantawa da shi a rayuwarki ba?
Ba zan taba manwata da ranar da mahaifina ya rasu ba, a kullum ina jin rashinshi sabo a zuciyata farin cikin da ba zan manta da shi ba shi ne; kullum da nake kallon mahaifiyata cikin lafiya da amincin Annabi.
Me ya fi sa ki farin ciki a rayuwa?
In ganni zaune cikin ‘yan uwana ga kuma jikokin gidanmu, ina jin farin ciki sosai shi ma.
Me za ki ce ga masu kokarin shiga harkar fim, har ma da wadanda suke ciki?
Ina so duk wacce za ta shiga harkar fim ta kasance da sanin iyayenta ta shigo domin alfarmar iyaye aka fi so fiye da daudar duniya. Mu kuma da muke cikinta Allah ya kara hada kanmu, Allah ya kara bamu zaman lafiya f i y e da yadda muke yanzu.
Me za ki ce da masoyanki?
Ina yi musu fatan alkairi, ina kuma kaunarsu fiye da yadda suke sona Allah ya bar kauna a tsakaninmu, Allah ya zaunar da kasarmu lafiya don Alfarmar Annabi.
Ko akwai wani kira da za ki yi ga gwamnati game da harkar fim?
Kira na ga gwamnati shi ne; kara wa kwarin giwa da mu da furodusashinmu da kuma daraktocinmu, duk wani kiran da muke yi ga gwamnati ne, sannan ina yin mata fatan alkhairi.
Me za ki ce da makarantar wannan shafi na Rumbun Nishadi da ita kanta Jaridar LEADERSHIP Hausa?
Ina yi musu fatan alkhairi Allah ya kara daga darajar wannan gidan Jarida ta LEADERSHIP Hausa, da kuma shafin Rumbun Nishadi, Allah ya kara muku kwarin gwiwa ga jajircewarku, kuma Allah ya cika muku burinku na alkhairi amen.
Ko kina da wadanda za ki gaisar?
Eh akwai su, ina mika gaisuwata musamman ga Ogana Isah Bawa Doro da kuma Yayana Ibrahim Bala, sannan Lawal Ibrahim Gungu, Balarabe Kabir, Sama’ila Abbah ina yi musu kyakkyawar gaisuwa ta musamman. Muna godiya Malama Hauwa Ni ma na gode.