Gwamnonin Arewa su 13 na Jam’iyyar APC, sun kade kai da fata cewa Shugabancin Nijeriya a zaben 2022 kawai ya tafi yankin Kudu, suna masu cewa, Shugaban Kasa Muhammadu, bai da wani dan takara a zaben fitar da gwani na jam’iyyar.
Bayanin nasu na fitowa ne bayan wata ganawar da suka yi da shugaban kasa a Abuja a ranar Litinin.
- Tsohon Sakataren Jam’iyyar APC Ya Fice Daga Jam’iyyar
- Ana Rade-Radin APC Ta Tsayar Da Ahmad Lawan A Matsayin Dan Takarar Masalaha
Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong, ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da ‘yan jarida a fadar shugaban kasa bayan fitowa daga taron, ya ce, tabbas gwamnonin Arewa sun cimma matsaya kan mulki ya tafi yankin Kudu.
Kazalika, ana sa ran gwamnonin za kuma su sake ganawa da kwamitin masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC duka a yau Litinin.
Shugaban Buhari dai ya gana da gwamnonin APC domin ganin an samu nasarar gudanar da zaben fitar da gwani cikin kwanciyar hankali ba tare da rikici ko samun wata tangarda ba.
Gwamnonin da suka halarci zaman sun hada da shugaban kungiyar gwamnonin APC kuma gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu da Shugaban kungiyar gwamnonin Arewa kuma gwamnan Jihar Filato, Simeon Lalong said gwamnan Jihar Jigawa, Abubakar Baduru da Babagana Zulum (Borno) da ragowar gwamnonin Arewa na Jam’iyyar APC.