Shugaban kungiyar ‘yan jarida (NUJ) ta kasa reshan Jihar Kano, Malam Abbas Ibrahim, ya bukaci cibiyoyi, hukumomi da kungiyoyin ci gaban al’umma na jihohi da makatakin kasa da su yi koyi da hukumar wayar da kan jama’a a kan rike kyawawan al’adun Nijeriya (NICO), kan shirya wa ‘yan jaridar Kano guda 50 bita na yadda ya kamata su rubuta labara wanda zai kawo zaman lafiya da tsaro da kwanciyar hankali a Nijeriya.
Malam Ibrahim ya bayyana hakan ne a lokacin bikin bude taron bitar ta kwana biyu wacce aka gabatar a dakin taro da ke gidan tunawa da Malam Aminu Kano da ke Unguwar Gwammaja cikin Jihar Kano.
- Sin Da Rwanda Sun Tsawaita Yarjejeniyar Hadin Gwiwa A Fannin Kiwon Lafiya Na Tsawon Shekaru 5
- Matar Aure Ta Bukaci Kotu Ta Raba Aurenta Da Mijinta Saboda Yawan Jima’i
Shugaban NUJ ya ce kungiyar na da tsari mai tsanani na hukunta dukkan wani dan kungiyar da ya nuna rashin iya aiki ko san zuciya a wannan aiki mai daraja na jarida.
Shi ma ana sa jawabin, babban sakataren NICO, Ado Muhammad Yahuza ya ce ‘yan jarida na da matukar muhimmanci a kowanne fanni na ci gaba musamman yanzu da ake bukatar samar da tsaro da kwanciyar hankali, wanda ya sa wannan hukuma ta shirya wa ‘yan jarida bita a wannan lokaci, domin su na da babbar gudunmawa wajen dakile tashi hankali da kawo zaman lafiya a ko wacce kasa