Yau 11 ga watan Satumba, shekaru 21 ke nan da aukuwar harin ta’addanci na ranar 11 ga watan Satumba a kasar Amurka, kuma a wannan rana, biranen Amurka da dama za su gudanar da tunawa daban-daban.
An lura cewa, Amurka ta fara daukar matakan yaki da ta’addanci ne a fadin duniya sakamakon harin ta’addancin da ya faru a shekarar 2001, wato Amurka tana fatan za ta kawar da ta’addanci ta hanyar daukar matakan soja, tare kuma da tilastawa sauran kasashen duniya, aiwatar da tsarin demokuradiya irin nata, amma hakika Amurka ta yi yaki kana ta tayar da tarzoma ne a Afghanistan da Iraki da Syria da Libya da sauran kasashe a cikin shekaru 21 da suka gabata, inda al’ummomi sama da dubban daruruwan suka rasu a fagen yaki, kana miliyoyin al’ummomi suka rabu da muhallansu.
Bugu da kari, a watan Agustan bara sojojin Amurka sun janye daga Afghanistan ba zato ba tsammani, lamarin dake alamta kawo karshen mamayar da sojojinta suka yi a Afghanistan na tsawon shekaru 20. Kwanan baya kakakin ma’aikatar tsaron gwamantin wucin gadi ta Afghanistan ya gaya wa wakilinmu na CMG cewa, gwamnatin wucin gadin kasar, ta kafa rundunar sojojin kasar mai zaman kanta tare da inganta ayyukanta, Sai dai duk da cewa Amurka ta kammala janye sojojinta daga kasar, amma har yanzu tana kai hare-haren soji da kutsawa cikin kasar ta Afganistan ta hanyar leken asiri ta sama da kuma dannawa cikin kasashen makwabta a cikin shekarar da ta gabata. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)