Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, ya bayyana cewar gwamnatin tarayya za ta kammala ginin gidajen yari uku wanda za su dauki fursinoni 3,000 ko wanne nan da watan Disambar shekarar nan.
Wadannan gidajen yarin sun hada da na Kano, Ribas da Abuja.
- Sojojin Somaliya Sun Kashe Mayakan Al-Shabab Sama Da 100
- Adadin Wadanda Suka Mutu Sakamakon Girgizar Kasa Mai Karfin Maki 6.8 Da Ta Afku A Lardin Sichuan Ya Kai 93
Aregbesola, ya bayyana hakan ne ga manema labarai bayan wani rangadin da ya kai gidan yarin da ke Karshi a Abuja, mai cin fursinoni 3,000.
Ya ce an kusa kammala wanda ke Kano yayin da aka kammala kaso 55 cikin 100 na aikin da ke Ribas da Abuja.
“Burina shi ne a samu guda uku na farko daga cikin ayyuka shida da za a kammala kafin wannan gwamnati ta kare.
“Muna da irin wannan wurin a Kano wanda ya kusa kammaluwa. Na yi imanin kafin watan Disamba, shugaban kasa ne zai kaddamar da shi.
“Wanda yake a Jihar Ribas ma ya kusa kai wa irin wannan matakin. Tare da goyon bayan shugaban kasa, wadannan biyu (Ribas da Abuja) za a kammala su nan da karshen shekara,” in ji shi.