- Ta Ziyarci Nijeriya Sau Biyu
- Yadda Ta Goyi Bayanmu Lokacin Yakin Basasa —Buhari
- Mulkin Mallaka Ne Ya Hada Mu Da Ingila—Dakta Shu’aibu
Wani Malami a Sashin Nazarin Harsuna da Al’adun Afirka a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Dakta Shu’abu Hassan, ya bayyana cewa, babbar alakar da ke tsakanin Nijeriya da Ingila, ta samo asali ce tun lokacin da Mango Park ya shiga kasar nan, wanda tun daga wannan lokaci aka fara samun dangantaka tsakanin Turawan Ingila da al’ummar Nijeriya.
Ganin yadda Mango Park ya ga yadda yanayin wannan yanki na Afirka yake, sai ya yi tunanin bunkasa yankunan, wanda daga nan ya fara kafa sansani, har zuwa lokacin da Turawa daga sauran nahiyoyi suka zo suka raba yankin kowa ya mallaki nasa.
A ta’aziyyarsa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, kasar Birtaniya a karkashin mulkin Sarauniya Elizabeth ta tsaya tare da Nijeriya a lokuttan da take fuskantar rikice rikice.
Ya ce, Birtaniya ta kasance a bangaren neman hadin kan Nijeriya a lokacin yakin basasa na shekarar 1967 zuwa 1970, ya ce, ta kuma ziyarci Nijeriya sau biyu a zamanin rayuwarta.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a yayin da ya je ziyarar ta’aziyya ga Ambasadan kasa Birtaniya a Nijeriya, Catriona Laing, a gidanta da ke Abuja ranar Asabar, ya kuma samu wakilcin Sakataren Gwamnatin tarayya Boss Mustapha.
Ya kuma kara da cewa, “Mun tabbagtar da kyakyawar alaka tsakaninmu da Sarauniyar. Muna kuma maraba da sabon Sarki da fatan zamu samu alaka kyakyawa kamar yadda muka yi da mahaifiyarsa”.
Yadda aka Ranstar Da Sarki Charles III
A ranar Asabar da ranar ne aka rantsar da Srrki Charles tare da mika masa dukkan abubuwan da al’ada ya tanada na mulki Ingila.
Ana asa ran binne Marigayya Sarauniya Elizabeth ranar Litinin 19 ga watan Satumba 2022 a Westminster Abbey, inda manyan shugabannin kasashen duniya za su halarta.
Marigayya Sarauniyar Ingila, Elizabeth II ta ziyarci kasashe rainon Birtaniya da dama a lokacin tana raye a lokacion da kasashen ke karkashin mulkin mallakar Ingila da kuma lokacin da suka samu ‘yancin kansu.
Tarihi ya nuna cewa, a Dakarun Ingila sun mamaye yankin Legas a shekarar 1851 daga baya kuma a shgekarar 1901 suka mayar da yankin a matsayin yankinsu na mulkin mallaka, sun cigaba da mulkar yankin da ake kira Nijeriya a yanzu har zuwa shekarar 1960 a lokacin da suka ba Nijeriya ‘yancin kai a tsawon wancan lokacin Sarki George BI ne ke a matsayin Sarki ga Nijeriya a tsarin mulkin da ake kira ‘Indirect rule’.
Bayan rasuwar Sarki George BI, ne sai Gimbiya Elizabeth Aledandra Mary ta dare karagar mulkiin Ingila a matsayin Sarauniya a ranar 6 ga watan Fabrairu na shekarar 1952, tana mai shekara 25 a duniya.
Daga lokacin da Nijeriya ta samu ‘yancin mulkin kai a shekarar 1960 har zuwa shekarar 1963 data zama Jumhoriyya, duk da Nijeriya ta samu mulkin kai amma tana nan a karkashin mulkin turawan Ingila inda ake daukar umarni da dokoki daga Sarauniyar Ingila, wannan yana faruwa ne duk kuwa da Dakta Nnamdi Azikiwe ke a matsayin shugaban kasa amma mara cikakken iko.
Wasu jam’iyyun siyasa a Nijeriya da wasu ‘yan Nijeriya masu yi wa kasa fatan alhairi basu aminta da wannan shirin ba na cewa, Sarauniyar Ingila ce za ta cigaba da zama shugabar kasa duk kuwa da ‘yancin mulkin kai da aka karba daga Ingila, a kan haka aka shiga matsa lamba don ganin an samu cikakken mulkin kai ba irin na jeka na yi ka ba, a kan haka ne aka samu nasarar samun cikakken ‘yanci shekara uku bayan bayan ‘yanci a ranar 1 ga wagtan Oktoba na shekarar 1968, daga wannan ranar Nijeriya ta fita daga kangin mulkin mallakar Ingila ta zama mai cin kashin kanta, kuma daga wannan ranar ba Sarauniyar Ingila ba ce Shugabar Nijeriya.
Duk da cewa, zamaninta a matsayin shugabar Nijeriya ya kare a ranar 1 ga watan Oktoba na shekarar 1968 amma Sarauniya Elizabeth ta ci gaba da tabbatar da hulda mai inganci a tsakaninta da Nijeriya har zuwa rasuwarta ranar 8 ga watan Satumba 2022.
Ziyarar Sarauniya Ta Farko Nijeriya A 1956
A matsayinta na kasar da ta yi wa Nijeriya mulkin mallaka Sarauniya Elizabeth ta ziyarci Nijeriya a shekarar 1952, don ganin yadda al’amurra ke tafiya, bayani ya nuna cewa a tsawon mulkin ta na shekara 70 a kan karagar Mulki Sarauniya Elizabeth ta samu nasarar ziyartar kasashe 50 cikin kasashen da Ingila ta yi wa mulki mallaka a ciki kuma ta ziyarci Nijeriya har sau biyu, a shekara 1956 da 2003.
A shekarar 1956, Sarauniya Elizabeth II ta ziyarci Nijeriya ne shekara 3 da hawanta karagar mulki a lokacin Sir James Robertson yake rike da matsayin Babban Gwamnan Nijeriya, a ziyarar data kawo ta yi kwanaki 20 a Nijeriya ta kuma zo ne tare da mijinta, Duke na Edinburgh. Inda ta iso Nijeriya a ranar 28 ga watan Janairu zuwa ranar 16 ga watan Fabrairu, inda ta zagaya sassan kasa tana duba ayyukan cigaba al’umma da ake gudanarwa da wadanda aka kammala. Sarakunan gargajiya na yankuna daban-daban sun shirya wa Sarauniya liyafa da hawan daba masu kayataiwa.
Wuraren da Sarauniya Elizabeth ta samu ziyara a shekarar 1956 data zo Nijeriya kusan shekara 3 bayan hawarta karagar Mulki tare da rakiyar mijinta, Mista Philip Mountbatten Duke na Edinburgh sun kuma sauka ne a filin jiragen sama na babbar birnin tarayyar Nijeriya, Legas, Babban Gwamnan Nijeriya na lokacin, James Robertson ya jagoranci tawagar tarbarta cikin kuma akwai Festus Okotie-Eboh; da Sarkin Legas na wancan lokacin Adenji-Adele II. A tsawon kwanaki 20 da ta yi a Nijeriya ta ziyarci jihar Kaduna, Kano da Inugu ta yi ibada a cocin ‘Cathedral Church of Christ’ na unguwar Marina da ke Legas, cocin da sanannen dan rajin kare hakkin al’umman nan mai suna Rabaren Samuel Ajayi Crowther ya gina, a yayin zuyara ta bayar da tallafin kujerun zama ga cocin.
Ta kuma ziyarci shahararren dan Nijeriya nan mai zane-zane, Ben Enwonwu a garin Benin inda ya yi alkawarin yin mutum-mutumin Sarauniyar, inda ya fara aiki gadangadan ya kuma kammala a shekarar 1957, aka kuma bayar da kyautar aikin ga Cibiyar Ajiye Kayan Tarihi na Landan.
Ziyararta Karo na Biyu
A ziyarar da Sarauniya Elizabeth II ta kawo Nijeriya karo na biyu, ta yi shi ne a shekarar 2003, a lokacin mulki tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.
A wannan karon ma ta zo ne tare da maigidanta Duke na Edinburgh daga ranar 3 zuwa 6 ga watan Disamba, babbar makasudin zuwanta ya hada da halartar taron shugabannin kasashe rainon Ingila na ‘[Commonwealth’ da aka yi ranar 5 ga watan Disamba 2003 a Abuja.
A wasikar da ta rubuto wa Shugaba Obasanjo, Sarauniya Elizabeth II ta bayyana cewa, ziyarar na daga cikin yadda Ingila ta muhimmantar da Nijeriya ne a fagen siyasar Afrika da duniya gaba daya. A yayin ziyarar Sarauniya Elizabeth ta kaddamar da taron shugabannin kasashe rainon Ingila, ta kuma halarci taruka ta kuma ziyarci kasuwanni a yankin Abuja.
An dai haifi Gimbiya Elizabeth Aledandra Mary ne a ranar 21 ga watan Afrilu ba shekarar 1926, ta zama Sarauniyar Ingila ne a shekarar 1952, bayan rasuwar mahaifinta Sarki George BII. Tana mai shekara 25 ta zama Sarauniya da shugaba ga ‘yantattun kasashe rainon Ingila 5 sun kuma hada da Birtaniya, Australia, New Zealand, Afrika ta Kudu, Pakistan, da kasar Sri Lanka. Kamar yadda ta zama Shugabar Nijeriya daga 1960 har zuwa watan Oktoba na 1963 a lokacin da Nijeriya ta zama jumhoriyya.
A daidai lokacin da ta dare karagar Mulki, daular Ingila ta fara rushewa musamman ganin yawancin kasashen da ingila ke yi wa mulkin mallaka suna yekuwar neman ‘yancin cin gashin kansu, inda kasar Ghana ta samu ‘yancin kanta a shekarar 1957 yayin da kasar Somalia da Nijeriya suka samu nasu ‘yancin kan a shekarar 1960.
A ziyarar ta karo na biyu, Sarauniya Elizabeth ta iso Nijeriya ne tana mai shekara 76, girma ya riga ya shigo mata, an manyanta, ta sauka ne a Abuja babbar birnin tarayyar Nijeriya. Cikin ayyukan da ta yi a yayin ziyarar da ta kawo Nijeriya sun hada da halartar taron shugabanin kasashe rainon Ingila karo na 18 inda ta jagoranci taron. Cikin manyan batutuwan da aka tattauna a taron sun hada da dakatar kasar daga kungiyar da kuma zaben dan kasar New Zealand, Don McKinnon a matsayin Babban Sakataren kungiyar.
Duk da cece-ku-ce da ke tattare da wasu bangare na rayuwar Sarauniya Elizabeth ta bar tahirin da aka dade ba a ga irinsa ba a duniya. Ta shafe shekara 70 da kwanaki 214 a kan karagar mulki, Sarauniya Elizabeth II ce mace ta biyu da ta fi kowacce dadewa a kan karagar mulki a tarihin duniya wannan kuwa yana zuwa ne bayan Sarauniya Louis DDIB ta kasar Faransa. Mutuwarta babbar darasi ne don kuwa ta samu damar ganin manya-manyan canje-canje a duniya a bangarorin rayuwa, al’adu da siyasar duniya. Babban danta Yarima Charles III ne ya gajeta.
Wanene Sarki Charles III?
Bayan rasuwar Sarauniya Elizabeth II, wadda ta kasance Sarauniyar da ta fi dadewa a kan karagar mulkin Ingila, yarima Charles, wanda shi ne babban danta cikin yara hudu data haifa da mijin ta Marigayi Yarima Philip.
An haifi Yarima Charles III wanda ake kuma kira da Charles Philip Arthur George ne a ranar 14 ga watan Nuwamba na shekarar 1948, ya yi zaman jiran gado tun shekarar 1958.
An haifi Yarima Philip ne a fadar Buckingham ya yi karatu a makarantar Cheam da Gordonstoun kamar dai mahaifinsa, Yarima Phillip ya kuma yi karatu a Timbertop da kuma makarantar Sakandire na Geelong da ke Bictoria, a kasar Australia.
Ya zama Yariman Wales a shekarar 1969, daga nan kuma ya wuce Jami’ar Wales a Aberystwyth, inda ya karanci yaren Welsh. Bayan shekara biyu ya dare kujerarsa a majalisar dokoki ta ‘House of Lords’, da kuma majalisar dattatawa ta ‘Upper house’ na Birtaniya.
Bayan kammala digirinsa a jam’iar Cambridge, Yarima Charles ya yi aiki da rundunar sojin Sama dana Ruwan Birtaniya a tsakanin shekarar 1971 zuwa 1976.
A shekarar 1981, Yarima Charles ya auri Lady Diana Spencer, wadda sunan ta ya koma Gimbiya Princess na Wales sun haifi yara biyu, William da Harry, wanda sune na biyu dana shida tsarin masu jiran gado na masarautar Ingilan.
A shekarar 1992 aurensu da Sarauniya Diana ya mutu, inda ya auri Camilla a shekarar 2005, aka kuma canza mata suna zuwa Duchess ta Cornwall sun zauna a cikin gidajen masaurautar Ingila da ake kira ‘Clarence House’, amma ana sa ran yanzu zai koma fadar Buckingham tunda ya zama Sarki. Sarki Charles yana da jikoki 5 dsaga yaransa biyu.
Ana sa ran kaddamar da Charles da Camilla, dukkansu masu shekara 75 a duniya a lokaci daya kamar yadda Sarauniya Elizabeth ta bukata.