Babbar jam’iyyar hamayya ta PDP a Nijeriya ta kafa kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Jam’iyyar, inda ta nada gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, matsayin babban daraktan yakin neman zaben shugaban kasar.
BBC ta rawaito cewa, wani sako da jam’iyyar ta wallafa a shafinta na Tuwita ta ce kwamitin wanda gwamnan jihar, Akwa Ibom Udom Emmanuel, ke shugabanta ya kunshi wasu gwamnonin da suka hada da gwamnan, Ribas Nyesom Wike, wanda ke ta kiraye-kirayen shugaban jam’iyyyar na kasa ya sauka daga mukaminsa.
- Nijeriya Ba Za Ta Bunkasa Ba Sai Da Ingantacciyar Wuta – TambuwalÂ
- Gwamna Wike Ya Karyata Batun Maka Atiku Da Tambuwal A Kotu
Jam’iyyar dai ta fada rikicin cikin gida ne tun bayan zaben fitar da gwani na jam’iyyar, zaben da ya bai wa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar nasara, matakin da bai yi wa gwamnan jihar, Ribas Nyensom Wike, dadi ba.
A makon da ya gabata ne dai Tambuwal, wanda ke shugabantar kungiyar gwamnonin jam’iyyar, da shugaban kwamitin amintatu na jam’iyyar Sanata Walid Jibrin, suka ajiye mukamansu, matakin da suka ce sun dauka domin samun masalaha a jam’iyyar.