ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nijeriya Ba Za Ta Bunkasa Ba Sai Da Ingantacciyar Wuta – Tambuwal 

by Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
4 years ago
Tambuwal

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sakkwato ya bayyana cewar akwai kalubale sosai a fannin samar da wutar lantarki a Kasar nan wanda ya zama wajibi idan a na son samun ci-gaba mai ma’ana a dauki kwararan matakai domin shawo kan matsalolin.

Ya ce fannin wuta na bukatar kwararru kuma gogaggun hannaye wadanda suke jajirtattu ta hanyar yin aiki da gaske domin shawo kan tarin manyan kalubalen da fannin ya jima yana fuskanta.
Ya ce Nijeriya za ta iya samun ci-gaba ne kadai a matsayin Kasa idan ta na da ingantacciyar wutar lantarki.

Ya ce kashe tsohuwar NEPA bai samu cikakkiyar nasara ba, har yanzu akwai kalubale sosai amma kuma za a iya shawo kan su idan Gwamnati da gaske take yi.

ADVERTISEMENT
  • ‘Yan Ta’adda Sun Tarwatsa Kauyuka 21 A Sakkwato

Gwamnan ya yi wannan bayanin ne a yayin da ya karbi bakuncin sabon Shugaban Hukumar Gudanarwar Kamfanin Wutar Lantarki na KAEDCO, Alhaji Abbas Muhammad Jega a Fadar Gwamnatin Sakkwato.
“Kasashe da dama sun yi, me zai hana mu ma mu yi? Ba za mu samu nasarar cika alkawulan mu ba, ba za mu gano damar da muke da ita ba idan ba mu gyara fannin wuta ba.” Ya bayyana.

Ya ce duk fannonin ci-gaba mafi yawa sun dogara ne ga samun wuta wanda a kan hakan ne ya ce Gwamnatinsa ta na goyon bayan bunkasa fannin wutar lantarki wanda a bisa ga wannan ne Gwamnatinsa ta kashe makuddan kudade wajen samar da na’urorin taransifoma da daga darajar layukan wuta a fadin Jihar.

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Gwamnan ya bukaci Kamfanin da su rika amfani da tsarin lissafin kudin wutar da aka ci maimakon hasashe ba tare da lissafi ba.Ya ce ta hanyar sanya na’urar mita, hasashen kudin wuta da ake yi zai ragu sosai, wanda hakan zai sa a samu gagarumar nasara a kokarin da ake yi na bunkasa fannin samar da wuta.

Tambuwal wanda ya ce yin amfani da tsarin biyan wutar da aka sha, shine mafi dacewa kamar yadda kamfanonin sadarwa ke yi wanda jama’a ke jin dadin tsarin, don haka me zai hana a yi shi a fannin wuta?” Gwamnan ya tambaya.

Ya ce yin hakan zai zama alfanu ga kamfanin domin za a gano kwastomomi na kwarai wadanda ke biyan wuta, haka ma wadanda ke biyan wuta za su gamsu kuma su ga alfanun biyan kudinsu kuma za rika cajinsu yadda ya kamata.

A jawabinsa Abbas Jega ya bayar da tabbacin cewar tattaunawar Kamfanin da Gwamnatin Jihar Sakkwato da jin bukatocin kwastomomin su ya karfafa fahimtar juna da samar da sakamako mai kyau a kakkarfan kamfani da samun wuta a kodayaushe a Jihar.

  • https://leadership.ng/tambuwal-rallies-north-west-businessmen-for-atiku/

Tambuwal, ya kuma bayyana nauyin matsalolin da aka gabatar tare da bayar da tabbacin za su kara tashi tsaye wajen magance matsalolin tare da kara inganta bayar da hasken wuta da rage korafe- korafen jama’a.

Tambuwal
Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
+ postsBio
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    2027:Cece-kuce Ta Barke Tsakanin Tinubu Da Atiku
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Yadda Rikici Ya Tsananta Tsakanin Dan Daba Da Malaman Addini A Sakkwato
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Dalilin Yawaitar Haduran Kwale-kwale A Yankin Sakkwato
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Atiku Ya Koka Kan Ƙaruwar Ta’addanci A Sakkwato

MASU ALAKA

Labarai

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu
Labarai

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Next Post
Saudiyya Ta Kama Mutumin Da Ya Yi Umrah Saboda Sarauniyar Ingila

Saudiyya Ta Kama Mutumin Da Ya Yi Umrah Saboda Sarauniyar Ingila

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.