Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta shaidawa taron manema labaru da aka saba yi Jumma’ar nan cewa, domin kare martabar kasar Sin, da moriyar tsaron kasar, gwamnatin kasar Sin ta yanke shawarar kakaba takunkumai kan jagororin kamfanonin Raytheon Technologies da Boeing Defense na kasar, saboda hannun da suke da shi a makaman da Amurka ta sayarwa yankin Taiwan na kasar Sin.
Bayan da Amurka ta sanar da shirinta na sayar da makaman da darajarusu ta dalar Amurka biliyan 1.106 ga yankin Taiwan a ranar 2 ga watan Satumba, kasar Sin ta bayyana cewa, za ta dauki kwararan matakai masu karfi don tabbatar da kare ‘yancin kai da maradunta na tsaro.(Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)