Gwamnatin Jihar Kano ta amince da biyan Naira miliyan 304 a matsayin alawus-alawus ga ma’aikata 287 na bangaren koyarwa na Jami’ar Yusuf Maitama Sule da suka cancanta.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Muhammad Garba ya fitar a Kano a yau Juma’a.
- Matsalolin Bashin Da Ake Bin Nijeriya
- Gwamnonin Arewa Maso Gabas Za Su Samar Da Kamfanin Zirga-zirgan Jirgin Sama
Ya bayyana cewa an ba da wannan amincewar ne a taron majalisar zartarwa na jihar na mako-mako.
Muhammad, ya kara da cewa za a rika biyan kudaden alawus-alawus din ma’aikatan ne daki-daki a kowane wata daga watan Oktoba.
“Za a biya Naira miliyan 297 ga ma’aikatan fannin koyarwa da aka tantance, yayin da aka kiyasta Naira miliyan 6.5 don a biya sauran ma’aikata ilimi 10 da a ka cire sunayensu bisa kuskure a biyan kudin da ya gabata.
“Majalisar ta kuma amince da sakin Naira miliyan 82.1 ga YMSU domin samar da ayyukan gyaran makarantar kai tsaye da kuma samar da kayan aiki a tsangayar kimiyya,” in ji shi.
Majalisar ta kuma amince da Naira miliyan 84.9 ga Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jiha (KUST) da ke garin Wudil.
Kudin don biyan dalibai ne da suka je shirin sanin makamar aiki a masana’antu, SIWES, da kuma alawus-alawus na zuwa saba’in makamar aiki koyarwa na zango biyu na 2019/2020 da 2021/2022 ga ma’aikatan ilimi da suka cancanta.