Yanzu haka dai rahotonnin da ke zuwa na cewa Gwamnonin jam’iyyar APC suna son a zabi daya daga cikin mutum uku da suke takarar neman tikitin Shugaban Kasa na jam’iyyar a tsakanin Tinubu, Osibanjo ko Amaechi.
Wannan matakin na sake rage adadin wadanda Gwamnonin ke son a zabi Dan Takaran Shugaban Kasa daga cikin su na zuwa ne kasa da ‘yan awanni da Gwamnonin suka Mika jerin sunayen mutum biyar ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da suke son a zabi daga cikinsu.
Wadanda gwamnonin suka fitar da safiyar yau Talata sun hada da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu; mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo; Rotimi Amaechi; Gwamna Kayode Fayemi da kuma gwamna Dave Umahi.
Daga bisani kuma suka sake zaftare biyu a cikinsu.
Duk da wannan matakin, ‘yan takara da suka hada da Kayode Fayemi da Yahaya Bello, sun dage cewa lallai suna cikin takarar daram.