• English
  • Business News
Friday, October 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wakilin Sin Ya Bukaci Kwamitin Sulhu Da Ya Soke Takunkuman Da Ya Kakabawa Sudan Ta Kudu

by CMG Hausa
3 years ago
Sin

Jiya Jumma’a mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Dai Bing, ya gabatar da wani jawabi yayin taron tattaunawa kan batun kasar Sudan ta kudu da kwamitin sulhun majalisar ya kira, inda ya bukaci kwamitin sulhun, da ya gaggauta soke takunkuman hana jigilar makamai da ya kakabawa kasar Sudan ta kudu.

Dai Bing ya bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, yanayin siyasa na Sudan ta kudu ya shiga wani sabon mataki mai muhimmanci, bangarori daban daban da suka sa hannu kan yarjejeniyar sake farfado da Sudan ta kudu, sun cimma ra’ayi daya da jadawalin tsawaita wa’adin mika mulki a kasar a watan jiya, shawarar da suka yanke ta dace da yanayin da ake ciki yanzu, kana za ta samar da zaman lafiya a kasar.

  • An Shirya Tattaunawar Tiangong Tsakanin ‘Yan Sama Jannatin Sin Da Matasan Afirka Cikin Nasara

Don haka, ya dace sauran kasashe duniya su fahimci matsalar da Sudan ta kudu take fuskantar, su fahimci shawarar da aka yanke, kada su yi amfani da shirya zabe a matsayin wata dabara ta daidaita daukacin hargitsi, kuma bai kamata a yi watsi da kokarin gudanar da tattaunawar shimfida zaman lafiya da bangarori daban daban na Sudan ta kudu suke yi ba.

Dai Bing ya kara da cewa, yanzu haka an yi nasarar yaye tare da jibge kashin farko na rundunar sojojin kasar Sudan ta kudu lami lafiya, wannan babban ci gaba ne da aka samu yayin tabbatar da yarjejeniyar sake farfado da kasar, matakin da ya alamta cewa, aikin shimfida zaman lafiya ta Sudan ta kudu, ya samu sabon ci gaba.

Amma takunkuman da kwamitin sulhun MDD ya kakabawa Sudan ta kudu, yana da illa ga rundunar sojojin Sudan ta kudu na samu makaman da take bukata domin gudanar da aikinta, don haka kasar Sin ta sake yin kira ga kwamitin sulhun majalisar, da ya mai da hankali kan bukatun Sudan ta kudu, ya gaggauta soke takukumnan da ya kakabawa kasar, don taimakawa Sudan ta kudu wajen kara karfinta na tabbatar da tsaro a kasar. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)

LABARAI MASU NASABA

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika
Daga Birnin Sin

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

October 16, 2025
Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa
Daga Birnin Sin

Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

October 16, 2025
Gaza
Daga Birnin Sin

Wane Ci Gaba Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza Ta Haifar?

October 16, 2025
Next Post
Sin

Fina-finan Nollywood 5 Da Suke Koyar Da Mu Hanyoyin Samun Kudi

LABARAI MASU NASABA

Shugaban Najeriya Ya Kaddamar Da Aikin Samar Da Ruwa Da Kamfanin Sin Ya Gudanar A Birnin Abuja

Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka Ta Bar Baya Da KuraAfuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka Ta Bar Baya Da Kura

October 17, 2025
Tsohon Ɗan Majalisar Bayelsa Ya Shawarci Jonathan Ya Guji Neman Takara A 2027

Tsohon Ɗan Majalisar Bayelsa Ya Shawarci Jonathan Ya Guji Neman Takara A 2027

October 17, 2025
Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

October 16, 2025
NAWIA

Ranar Abinci Ta Duniya: NAWIA Ta Tallafawa Mata 114  Da Kayan Aikin Gona A Zamfara

October 16, 2025
Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

October 16, 2025
Gaza

Wane Ci Gaba Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza Ta Haifar?

October 16, 2025
Tsohon Ɗan Wasan Dambe, Ricky Hatton Ya Rataye Kansa

Tsohon Ɗan Wasan Dambe, Ricky Hatton Ya Rataye Kansa

October 16, 2025
Alkaluman Jin Ra’ayi na CGTN Sun Shaida Amincewar Al’umma Da Karfin Tattalin Arzikin Kasar Sin

Alkaluman Jin Ra’ayi na CGTN Sun Shaida Amincewar Al’umma Da Karfin Tattalin Arzikin Kasar Sin

October 16, 2025
Masu Bincike Na Sin Sun Kera Wani Dan Karamin Mutum Mutumin Hannu Da Zai Taimaka Wajen Gwaje-wajen Kimiyya

Masu Bincike Na Sin Sun Kera Wani Dan Karamin Mutum Mutumin Hannu Da Zai Taimaka Wajen Gwaje-wajen Kimiyya

October 16, 2025
Tinubu

Shugaban Ƙasa Zai Sake Nazari Kan Mutanen Da Aka Yi Wa Afuwa

October 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.