Cibiyar Akantoci ta kasa ICAN ta bayyana cewa ba za ta iya hukunta tsohon Akanta-Janar na kasa da aka dakatar ba, Ahmed Idris kan zargin badakalar naira biliyan 80, domin Shi, ba mambanta ba ne.Â
A cikin sanarwar da Cibiyar ta fitar a jiya Litinin na mayar da martani kan wata wasikar da wata kungiya mai zaman kanta HEDA ta fitar, inda ta bukaci Cibiyar ta ICAN da ta gurfanar da bincike tare da hukunta Idris wanda a yanzu hukumar EFCC ke kan gudanar da bincike a kansa kan maganar badakalar naira biliyan 80.
Kungiyar ta HEDA ta kuma bukaci Cibiyar ta ICAN da ta zurfafa bincike a kan Idris domin ta hukunta shi yadda ya dace.
Magatakardan da kuma babban Jami’in Cibiyar ta ICAN Farfesa Ahmed Kumshe a martaninsa kan wasikar ta HEDA ya ce, Cibiyar ba ta da hurumin hukunta shi domin Idris ba ya daya daga cikin ‘ya’yanta.