Bakwai daga cikin ‘yan takarar da suke neman tikitin shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC sun yi watsi da matakin gwamnonin APC na ware sunan mutum biyar da tura wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da nufin ya zabi daya cikinsu.
Mutum biyar da gwamnonin suka zaba su ne, YemiOsinbajo da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti sai Rotimi Amaechi da gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi.
- Gwamnonin APC Sun Kara Rage Adadin ‘Yan Takarar Shugaban Kasa Daga 5 Zuwa 3
- Zaben APC: ÆŠaya Daga Cikin Deliget Daga Jihar Jigawa Ya Rasu A Abuja
A sanarwar da suka fitar a Abuja, ‘yan takara bakwai sun yi tir da ware mutum biyar a cikinsu tare da cewa suna cikin takarar har yanzu.
‘Yan takara bakwai din sun hada da gwamnan Kurus Ribas, Ben Ayade; tsohon karamin ministan ilimi, Emeka Nwajiuba; tsohon ministan Kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu; tsohon gwamnan Imo, Sanata Rochas Okorocha da kuma fitaccen dan kasuwar nan, Tein Jack-Rich.
‘Yan takaran sun ce ba a tuntubesu ba kafin daukan wannan matakin don haka ba su amince da matakin Gwamnonin APC din ba, sun misalta matakin a matsayin abun kunya da kokarin tauye hakkin wasu ‘yan takara musamman na yankin Kudu Maso Gabas da Kudu Maso Kudu.
Suka ce, “Magoya bayanmu da daman gaske suna ta kiranmu da turo mana sakon karta kwana suna tambayarmu ya aka yi haka aka cire sunayenmu. Don haka mun yi tir da matakin Gwamnonin.”