Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi ya gabatar da jawabi game da huldar Sin da Amurka, yayin taron kungiyar al’ummun Asiya da aka yi jiya, a hedkwatar kungiyar dake binin New York na Amurka.
A cewar Wang Yi, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya riga ya fayyace hanyoyin da suka dace na kyautata huldar Sin da Amurka, wadanda suka hada da mutunta juna da hakuri da bambance-bambace da hadin gwiwar moriyar juna.
Ya kara da cewa, wadannan ka’idoji 3 muhimmai ne da huldar Sin da Amurka ta ginu a kai cikin sama da rabin karni, haka kuma su ne hanyoyi mafi dacewa na inganta mu’amala tsakanin manyan kasashen biyu a wannan zamani.
Ya kuma jaddada cewa, batun Taiwan ya fi muhimmanci ga kasar Sin, haka kuma amincewa da manufar kasar Sin daya tak a duniya, ita ce tubalin huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Amurka. (Fa’iza Mustapha)