A kwanan baya, majalisar hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa (IAEA), ta gudanar da wani taro don tantance batun hadin gwiwar kasashen Amurka, da Birtaniya, da Australiya, ta fuskar jiragen ruwan yaki dake tafiya a karkashin ruwa, masu yin amfani da makamashin nukiliya. Wannan taro ya kasance karo na 4, da kasashe mambobin IAEA suka cimma matsaya, wajen sake tantance batun da ya shafi hadin kan kasashen Amurka, da Birtaniya, da kuma Australiya, a fannin aikin soja, inda ya hana su zartas da shirin hadin gwiwarsu ta hanyar sa hannu kan wata yarjejeniya kawai.
Idan ba a manta ba, a shekara daya da ta gabata, kasashen Amurka, da Birtaniya, da Australiya, sun kulla wata yarjejeniyar hadin gwiwa mai lakabin AUKUS, inda bangarorin Amurka da Birtaniya, suka yi shirin kera wasu manyan jiragen ruwan yaki dake tafiya a karkashin ruwa, masu yin amfani da makamashin nukiliya guda 8, da niyyar sayar da su ga bangaren Australiya.
Sai dai niyyarsu ta gamu da kin amincewa sosai daga sassan kasa da kasa. Saboda hadin gwiwar kasashen 3 a wannan fanni za ta haddasa bazuwar sinadaran makaman nukiliya a duniya, lamarin da zai haifar da babbar barazana ga tsaron duniya. (Bello Wang)