Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Ahmad Sani Yarima, ya ce bai janye wa kowa takararsa ba.
Yarima ya ce ya je dandalin Eagle Square a matsayin guda cikin masu zawarcin takarar shugaban kasa a Jam’iyyarsu ta APC.
BBC Hausa ta tambaye shi cewa me zai ce kan batun mutum biyar da aka ce sunayensu aka bayar a matsayin masu yin takara inda ya ce “ai wannan an ce ne, amma ka ganni nan na zo takara. “Saboda haka an ce an ce ba gaskiya ba ne, da gaskiya ne da ba a ganni a nan ba.”
Ya kara da cewa babu wanda ya tuntube shi batun janyewa. Ya ce a halin yanzu suna jira ne a fara zabe.