Shugaban kasar Malawi Lazarus Chakwera, ya jinjinawa matakin kasar Sin, na yafewa wasu kasashen Afirka 17, basussuka marasa ruwa da take bin su.
Da yake bayyana hakan a ranar Alhamis, a gefen babban taron MDD karo na 77 dake gudana, shugaba Chakwera ya ce “Na yabawa kasar Sin bisa yadda take jagoranci abun misali, inda ta cika alkawarin da ta dauka yayin taron dandanlin raya hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka na FOCAC da ya gudana a bara, na yafewa kasashe Afirka 17 bashi maras ruwa da take bin su”.
Shugaban na Malawi ya kara da cewa, ya kamata a cika alkawarin yin tafiya tare da kowa, a kuma yi hakan a fayyace, ba wai ta maganar fatar baki kadai ba.
Ya ce “Idan har mu iyali guda ne na MDD, ya zama wajibi mu ajiye batun siyasa, mu rungumi karin tallafi wajen warware matsalolin mu”. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp