• English
  • Business News
Saturday, July 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ministan Wajen Kasar Sin Ya Halarci Taron Ministocin BRICS

by CMG Hausa
3 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Ministan Wajen Kasar Sin Ya Halarci Taron Ministocin BRICS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A ranar Alhamis ne babban dan majalissar gudanarwa, kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya halarci taron ministocin kungiyar BRICS, a gefen babban taron MDD karo na 77, dake gudana a birnin New York na Amurka. 

Da yake tsokaci yayin taron, Wang Yi ya ce a watan Yunin bana, an gudanar da taron shugabannin kungiyar BRICS karo na 14 cikin nasara, wanda kuma ya ba da damar bude sabon fagen hadin gwiwa tsakanin kasashe mambobin kungiyar.

  • Wang Yi Ya Yi Bayani Kan Ganawar Shugabannin Kasashen BRICS Karkashin Jagorancin Xi

Ya ce a yanzu haka, yanayin harkokin duniya na cike da rashin tabbas da sarkakiya, yayin da kalubale daban daban ke ci gaba da fuskantar sassan kasa da kasa. Wang Yi ya kara da cewa, tsaro shi ne jigon ci gaba, yayin da kuma ci gaba ke tabbatar da tsaro.

A cewar sa, kamata ya yi kasashe mambobin kungiyar BRICS su mara baya sosai, ga fannonin da ka iya ingiza ci gaba, yayin da suke halartar babban taron MDD, su kuma shigar da sabon kuzari ga ayyukan dake cikin ajandar ci gaba mai dorewa ta MDD, ta nan da shekarar 2030.

Kaza lika ya kamata a yi watsi da duk wata manufa ta rarrabuwa, da warewa, da shingayen fasahohi, maimakon hakan a tabbatar da gina budadden tattalin arzikin duniya, domin cimma nasarar bunkasar duniya tare, da kare muhalli da kare lafiyar al’umma.

Labarai Masu Nasaba

Philippines Na Zama Tushen Tashin Hankali A Tekun Kudancin Kasar Sin

Kasar Sin Ta Gano Ma’adanin Yuraniyom Mafi Daraja A Karkashin Kasa Mai Zurfi

Wang Yi ya kuma bayyana cewa, taron kungiyar G20 na Bali na karatowa, don haka ya kamata a karfafa tuntubar juna, da kyautata tsare tsare don kare halastaccen hakki, da moriyar kasashe masu samun saurin bunkasuwa, da kasashe masu tasowa.

Bugu da kari, ya dace a bibiyi managartan tsare tsaren da shugabannin kungiyar BRICS suka samar, a aiwatar da sakamakon taron, a cimma matsaya guda, da rungumar karfin hali irin na kungiyar BRICS. (Saminu Alhassan)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Shugaban Malawi Ya Jinjinawa Matakin Kasar Sin Na Yafewa Kasashen Afirka Basussuka Marasa Ruwa

Next Post

Tsananin Zafin Kaye A ZaÉ“en Fidda Gwani Yasa Wike Sambatu – Babba Mazoji

Related

Philippines Na Zama Tushen Tashin Hankali A Tekun Kudancin Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Philippines Na Zama Tushen Tashin Hankali A Tekun Kudancin Kasar Sin

3 hours ago
Kasar Sin Ta Gano Ma’adanin Yuraniyom Mafi Daraja A Karkashin Kasa Mai Zurfi
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Gano Ma’adanin Yuraniyom Mafi Daraja A Karkashin Kasa Mai Zurfi

4 hours ago
Yawan Jarin Waje Da Sin Ta Samu Ya Haura Dalar Amurka Biliyan 700
Daga Birnin Sin

Yawan Jarin Waje Da Sin Ta Samu Ya Haura Dalar Amurka Biliyan 700

5 hours ago
Sin Ta Yi Allah Wadai Da Hare-Haren Da Isra’ila Ta Kai Syria
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Allah Wadai Da Hare-Haren Da Isra’ila Ta Kai Syria

6 hours ago
Hanya Mai Salon Musamman Da Kasar Sin Take Bi Wajen Raya Harkokin Kudi
Daga Birnin Sin

Hanya Mai Salon Musamman Da Kasar Sin Take Bi Wajen Raya Harkokin Kudi

7 hours ago
Peng Liyuan Ta Halarci Bikin Hada Hannun Matasa Da Yaran Sin Da Amurka Na Shekarar 2025
Daga Birnin Sin

Peng Liyuan Ta Halarci Bikin Hada Hannun Matasa Da Yaran Sin Da Amurka Na Shekarar 2025

17 hours ago
Next Post
Tsananin Zafin Kaye A ZaÉ“en Fidda Gwani Yasa Wike Sambatu – Babba Mazoji

Tsananin Zafin Kaye A Zaɓen Fidda Gwani Yasa Wike Sambatu - Babba Mazoji

LABARAI MASU NASABA

Dangote

Dalilin Da Ya Sa Dangote Ya Jinjina Wa Hukumar NPA

July 18, 2025
Philippines Na Zama Tushen Tashin Hankali A Tekun Kudancin Kasar Sin

Philippines Na Zama Tushen Tashin Hankali A Tekun Kudancin Kasar Sin

July 18, 2025
2027: Atiku, Obi Da Amaechi Za Su Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Takarar Shugaban Kasa A ADC

2027: Atiku, Obi Da Amaechi Za Su Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Takarar Shugaban Kasa A ADC

July 18, 2025
Kasar Sin Ta Gano Ma’adanin Yuraniyom Mafi Daraja A Karkashin Kasa Mai Zurfi

Kasar Sin Ta Gano Ma’adanin Yuraniyom Mafi Daraja A Karkashin Kasa Mai Zurfi

July 18, 2025
majalisar kasa

Kirkirar Sabbin Jihohi Da Kananan Hukumomi Sun Dabaibaye Sauraron Jin Ra’ayoyin Gyaran Tsarin Mulki

July 18, 2025
Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Lallasa Zambia Da Ci 5-0

Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Lallasa Zambia Da Ci 5-0

July 18, 2025
Yawan Jarin Waje Da Sin Ta Samu Ya Haura Dalar Amurka Biliyan 700

Yawan Jarin Waje Da Sin Ta Samu Ya Haura Dalar Amurka Biliyan 700

July 18, 2025
A Karon Farko Dino Melaye Ya Bayyana A Gaban Kotu A Matsayin Lauya

A Karon Farko Dino Melaye Ya Bayyana A Gaban Kotu A Matsayin Lauya

July 18, 2025
Biyan Tukuici: Gwamna Yusuf Ya Ƙaddamar Da Tallafin Naira 50,000 Ga Mata 5,200 Duk Wata A Kano

Biyan ‘Yan Fansho Naira Biliyan 22: NUP Da NLC Sun Bukaci A Yi Koyi Da Gwamna Abba

July 18, 2025
Sin Ta Yi Allah Wadai Da Hare-Haren Da Isra’ila Ta Kai Syria

Sin Ta Yi Allah Wadai Da Hare-Haren Da Isra’ila Ta Kai Syria

July 18, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.