Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa tana cigaba da kokarin bude Wuraren sayar da iskar Gas (LNG) a tsakanin al’ummomi da dama, domin magance tashin farashin iskar gas a kasar nan.
Dr. Mohammed Ibrahim, shugaban shirin fadada iskar gas (NGEP) ya bayyana haka a taron shekara-shekara na 2022 na kungiyar masu sayar da iskar gas ta Nijeriya (NALPGAM) a Fatakwal, jihar Ribas a ranar Laraba.
Taken taron shi ne “Dorewar iskar Gas (LPG) da yadda zamani ke tunkararta a yau da kullum.”
Ibrahim ya ce Gwamnatin Tarayya ta mayar da hankali sosai wajen ganin an samar da LPG ga ‘yan Nijeriya kuma a kan farashi mai sauki nan gaba kadan.
Ibrahim ya kara da cewa Nijeriya ba ta da wani shirin fara fitar da iskar Gas zuwa kasashen waje a lokacin da kasarta ke cikin fuskantar kalubalen sarrafa iskar Gas din.
A cewarsa, kasar na da wadatar LNG a cikin tafkin Dahomy, N tafkin Delta, tafkin Bida, tafkin Gongola da tafkin Chadi, da dai sauransu.