Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya bayyana ‘yan bindiga a matsayin dabbobi, inda ya ce sun cancanci a kashe su.
Da yake magana yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na TVC, Matawalle ya ce gwamnatin jihar ta dauki matakai da dama wajen dakile ayyukan ta’addanci amma matakan ba su yi nasara dari bisa dari ba.
Gwamnan ya ce, “Mun yi iya kokarinmu. Mun dauki matakai da dama wajen dakile ta’addanci a jihar, wasu matakan an yi nasara mai yawa.
“Mun yi sulhu da su. Mun datse hanyar sadarwa. Mun yanke sayar da kayan abinci kuma mun ga nasara acikin wasu, amma ba kashi dari bisa dari ba.
‘Yan bindigar na tsoron kungiyar ‘yan banga ta ‘Yansakai, sabida suna amfani da bindiga mai amfani da fulogi a Matsayin harsashi. ‘Yan bindigan suna tsoron harbin fulogi, Sabida yana fatattaka su, sannan ya raba jikinsu gida biyu.
“Suna ganin Yansakai a matsayin mafi azabar mutane. Na san dalilin da ya sa na ba da wannan umarnin kuma na yi nasara da wannan umarnin da na bayar. Hukuncin kisa zai yi aiki. Na sanya hannu. Duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci doka.
“Abin da ya sa na ce kowa ya mallaki makami shi ne, ‘yan bindigar kamar dabbobi ne. Ta yaya za ka ga wani yana noma, sai ka je kawai ka kashe shi? Idan muka ce, kada mutanenmu su mallaki makami, wa zai je ya tunkari ‘yan bindigan in ba jama’armu ba! Masu cewa umarnin ba daidai ba ne, me ya sa ba za su iya zuwa su ceci mutanenmu ba?
“A matsayina na gwamna, ba zan iya nade hannuna in ga ana kashe mutanena kowace rana ba. Ba zai yiwu ba. Yana daga cikin muhimman ayyukan da ke kan gwamna na kare rayuka da dukiyoyin al’ummarsa.”