A ranar Litinin ne masu ababen hawa da sauran masu amfani da hanya suka yi dandazo a kan babbar hanyar Lokoja zuwa Abuja yayin da ambaliyar ruwa ta mamaye hanyar da ake gina sabuwar gada a kewayen garin Kotonkarfei da ke jihar Kogi.
Masu ababen hawa na shafr sa’o’i da dama, lamarin da ya haifar da cunkoson ababen hawa wanda fara tun daga ka titin Lokoja-Koton-Karfe.
- Ina Sukar Buhari Kan Gazawarsa Na Kawo Karshen Kashe-Kashen Jama’a A Binuwe
- Kungiyoyin Kasa Da Kasa Sun Yi Fatan Gudanar Da Babban Taron Wakilan JKS Karo Na 20 Cikin Nasara Yayin Da Kasar Sin Ke Bikin Ranar Kafuwar Kasa
Motoci da dama sun makale saboda babu wata hanya ta daban da za su bi.
Wani direban mota mai suna Mallam Ahmadu wanda ya shafe sa’o’i a kan hanyar, ya ce akwai fargaba a tsakanin matafiya.
An jibge ‘yansanda da sojoji da jami’an hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) da kuma matasa masu aikin sa kai zuwa wurin da lamarin ya faru kafin komai ya daidai.
Sai dai wani shaidar gani da ido ya ce abin da ke faruwa kan gadar Murtala Muhammadu da ke unguwar Jamata na iya daukar lokaci mai tsawo kafin a kawar da cunkoso saboda rashin hakurin da masu ababen hawa ke yi sun mamaye duk wata hanya lamarin da ke da wahala a samu saukin zirga-zirgar ababen hawa.