• Leadership Hausa
Sunday, January 29, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Kotu Da Ɗansanda

Mai Gida Ya Kashe ‘Yar Hayar Gidansa Da Wuka A Ondo

by Sadiq
4 months ago
in Kotu Da Ɗansanda
0
Mai Gida Ya Kashe ‘Yar Hayar Gidansa Da Wuka A Ondo

An gurfanar da Abidemi Oguntuyi mai shekaru 23 a gaban wata kotun majistare da ke Akure, babban birnin Jihar Ondo, bisa zarginsa da daba wa wata mata wuka mai suna Abiye mai shekaru 40 a duniya. 

Marigayiyar, wadda ke zaman haya a gidan wanda ake zargin, an ce ta yi kokarin sasanta rikicin da ya barke tsakanin Oguntuyi da dan uwansa a lokacin da aka daba mata wuka a wuyanta da wasu sassan jikinta.

  • Ambaliyar Ruwa Ta Shanye Titin Abuja Zuwa Lakwaja
  • Kungiyoyin Kasa Da Kasa Sun Yi Fatan Gudanar Da Babban Taron Wakilan JKS Karo Na 20 Cikin Nasara Yayin Da Kasar Sin Ke Bikin Ranar Kafuwar Kasa

An gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bisa laifuka biyu na kisan kai da kuma yunkurin kisan kai.

Lamarin ya faru ne a ranar 6 ga watan Satumba, 2022, da misalin karfe 11:00 na safe a unguwar Akungba-Ibaka Akoko, karamar hukumar Akoko ta Kudu maso Yamma a jihar.

Laifukan sun ci karo da sashe na 319 da 355 na dokar laifuka ta Jihar Ondo, karkashin sashe na 37 na dokar 2006.

Labarai Masu Nasaba

NIS Ta Kubutar Da Mutum 45 Daga Masu Safarar Mutane A Jigawa

Mahaifin Da Ake Zargi Da Lalata Da ‘Yarsa Ya Gurfana A Kotu

Simon Wada, dan sanda mai shigar da kara, ya bukaci da a tsare wanda ake kara a gidan gyaran hali na Olokuta yayin da kotu ke jiran shawarar daraktan kararrakin jama’a, DPP.

Lauyan wanda ake tuhuma, Adeola Kayode, ya yi bukaci a dage shari’ar don ba shi damar shigar da kara a rubuce ga mai gabatar da kara.

Alkalin kotun, D.S. Sekoni, ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake zargin a hannun ‘yansanda har zuwa lokacin da za a yanke hukunci sannan ya dage shari’ar har zuwa ranar 7 ga Oktoba, 2022, domin yanke hukunci.

Tags: AlkaliGidan HayaHukunciKisaKotuRabon FadaRikiciWukaZargi
Previous Post

Ambaliyar Ruwa Ta Shanye Titin Abuja Zuwa Lakwaja

Next Post

Dan Kwallo Ya Mutu Ana Tsaka Da Wasa A Filin Kwallo A Legas 

Related

NIS Ta Kubutar Da Mutum 45 Daga Masu Safarar Mutane A Jigawa
Kotu Da Ɗansanda

NIS Ta Kubutar Da Mutum 45 Daga Masu Safarar Mutane A Jigawa

1 day ago
Mahaifin Da Ake Zargi Da Lalata Da ‘Yarsa Ya Gurfana A Kotu
Kotu Da Ɗansanda

Mahaifin Da Ake Zargi Da Lalata Da ‘Yarsa Ya Gurfana A Kotu

1 day ago
Ana Tuhumar Mutum 8 Da Aikata Luwadi Da Fashi A Zamfara
Kotu Da Ɗansanda

Ana Tuhumar Mutum 8 Da Aikata Luwadi Da Fashi A Zamfara

1 day ago
An Kama Wani Da Ake Zargi Da Hannu A Harin Jirgin Kasan Kaduna Zuwa Abuja
Kotu Da Ɗansanda

An Kama Wani Da Ake Zargi Da Hannu A Harin Jirgin Kasan Kaduna Zuwa Abuja

1 day ago
An Yanke Wa Wata Mata Hukuncin Daurin Shekara 6 Kan Safarar Miyagun Kwayoyi
Kotu Da Ɗansanda

An Yanke Wa Wata Mata Hukuncin Daurin Shekara 6 Kan Safarar Miyagun Kwayoyi

1 week ago
Mutum 25 Ne Suka Bace Cikin Wata 6 A Jihar Abia — ‘Yan Sanda
Kotu Da Ɗansanda

‘Yan Ta’addar Da Suka Yi Garkuwa Da DPO A Jihar Filato Sun Sake Shi

2 weeks ago
Next Post
Dan Kwallo Ya Mutu Ana Tsaka Da Wasa A Filin Kwallo A Legas 

Dan Kwallo Ya Mutu Ana Tsaka Da Wasa A Filin Kwallo A Legas 

LABARAI MASU NASABA

Tsokaci Kan Dukan Da Wasu Maza Ke Wa Matansu

Tsokaci Kan Dukan Da Wasu Maza Ke Wa Matansu

January 28, 2023
Babu Wata Baraka Tsakanina Da Buhari – Tinubu

Babu Wata Baraka Tsakanina Da Buhari – Tinubu

January 28, 2023
‘Yansanda Sun Kama Kasurguman ‘Yan Bindiga 2, Sun Ceto Mutane 7, Sun Kwato 2.1m Kudin Fansa

‘Yansanda Sun Kama Kasurguman ‘Yan Bindiga 2, Sun Ceto Mutane 7, Sun Kwato 2.1m Kudin Fansa

January 28, 2023
Son Rai Da Rashin Cancantar Jarumai Ke Gurbata Al’adu A Fina-finanmu –Daushe

Son Rai Da Rashin Cancantar Jarumai Ke Gurbata Al’adu A Fina-finanmu –Daushe

January 28, 2023
Mataimakin Wakilin Kasar Sin Dake MDD Ya Yi Kira Ga Kasashen Duniya Da Su Taimakawa Mali Kara Karfin Yaki Da Ta’addanci

Mataimakin Wakilin Kasar Sin Dake MDD Ya Yi Kira Ga Kasashen Duniya Da Su Taimakawa Mali Kara Karfin Yaki Da Ta’addanci

January 28, 2023
Bikin Bazara Na Gargajiyar Kasar Sin Ya Kara Azama Kan Farfadowar Tattalin Arzikin Duniya

Bikin Bazara Na Gargajiyar Kasar Sin Ya Kara Azama Kan Farfadowar Tattalin Arzikin Duniya

January 28, 2023
Noman Kankana Na Kara Bunkasa A Jihar Jigawa

Noman Kankana Na Kara Bunkasa A Jihar Jigawa

January 28, 2023
Masani: Sin Za Ta Iya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Bunkasa Ci Gaban Duniya A Shekarar 2023

Masani: Sin Za Ta Iya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Bunkasa Ci Gaban Duniya A Shekarar 2023

January 28, 2023
Matsalolin Da APC Ta Jefa ‘Yan Nijeriya Ya Kamata Su Zama Darasi -Jarman Makarfi

Matsalolin Da APC Ta Jefa ‘Yan Nijeriya Ya Kamata Su Zama Darasi -Jarman Makarfi

January 28, 2023
Dole A Hada Karfi Wajen Dakile Bazuwar Makamai A Afirka –Buhari

Ba Don A Wahalar Da Talaka AKa Sauya Kudin Nijeriya Ba —Buhari 

January 28, 2023
ADVERTISEMENT
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.