Mambobin kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP sun isa Fatakwal, babban birnin jihar Ribas a yammacin ranar Talata, domin ganawa da gwamna Nyesom Ezenwo Wike.
Wakilan kwamitin amintattun karkashin jagorancin mukaddashin shugaban kwamitin kuma tsohon shugaban majalisar dattawa, Adolphus Wabara, sun isa gidan gwamnatin jihar Ribas, wurin taron da misalin karfe 2:00 na rana, sannan kuma kai tsaye suka shiga ganawar sirri da Wike.
Wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP a jihar, wadanda har yanzu suke biyayya ga gwamnan, ciki har da tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai, Prince Chibudom Nwuche, dattijon jihar, Cif Ferdinand Anabraba da shugaban jam’iyyar PDP a jihar, Ambasada Desmond Akawor duk angansu sun hallara wurin taron.
LEADERSHIP ta tattaro cewa, an bayyana cewa za a yi wa manema labarai bayani kan taron da zarar an kammala taron.
Cikakkun bayanai Daga baya…