Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bukaci masu aikin nazarin albarkatun karkashin kasa dake aiki a lardin Shandong na gabashin kasar, da su ci gaba da kyakkyawan aikin da suke yi, tare da taka rawar gani a aikin hako karin ma’adanai.
Shugaba Xi ya yi wannan kira ne a ranar Lahadi, cikin wata wasika da ya aike ga tawagar ma’aikatan hukumar nazarin albarkatun karkashin kasa da albarkatun ma’adanai ta lardin Shandong. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp