Sani Gyadi-Gyadi, DPO din ‘yansanda na yankin Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna, an sako shi bayan ya shafe sama da watanni uku a tsare a hannun ‘yan bindiga.
An sace shi ne a watan Yuni a Birnin Gwari a kan hanyarsa ta komawa bakin aiki a Birnin-Gwari, bayan ya sauyin wajen aiki.
- Yara 3 Sun Tsere Daga Maboyar ‘Yan Bindiga Yayin Da Suke Barci A Abuja
- Buhari Ya Umarci Manyan Hafshoshin Soji Da Su Koma Yankin Arewa Maso Gabas
An ce an sako dan sandan ne bayan biyan karin kudin fansa ga wadanda suka yi garkuwa da shi.
An ce abokai da ‘yan uwan jami’in, a watan Satumba, suka bayar da gudunmuwar Naira miliyan 7 ga ‘yan bindigar.
Sai dai an ce ‘yan bindigar sun bukaci karin kudi da babura, yayin da wanda ya je kai kudin fansar barayin suka yi awon gaba da shi.
A watan Satumba, dangin Gyadi-Gyadi su ma sun roki gwamnatin tarayya da ta taimaka wajen ganin an sako shi daga hannun masu garkuwa da mutanen.
“Jami’in ya gaya min cewa duk ruwan sama na bana a kansa ya sauka kuma ba shi da lafiya,” in ji daya daga cikin danginsa.
Duk da cewa Mohammad Jalige, kakakin rundunar ‘yansandan Kaduna bai tabbatar da sakin DPO din ba, wata majiya ta ‘yansanda ta tabbatar da cewa an sake shi a ranar Laraba kuma an kai shi asibiti.
Sai dai wani dan sanda da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da sakin DPO din.
Ya kara da cewa ‘yan bindigar sun sako jami’in da suka sace a ranar Laraba bayan an biya su karin kudin fansa.
Jami’in ya kara da cewa an kai DPO asibiti sakamakon yanayin lafiyarsa.