Kwamishinan rundunar ‘yansanda a jihar Adamawa, CP Sikiru Akande, ya gabatar da mutum 44, da jami’an rundunar su ka kame, gaban manem alabarai a Yola, bisa zargin aikata miyagun ayyuka a jihar.
Da yake gabatar da mutanen kwamishinan ya ce rundunar ta kuma kame mutanen da bindigogi hadi da kirar Ak-47, alburusai masu rai, kwamfita (Laptop), kananan bindigogi, motoci biyu da bakin man na mota, keke-nape da wasu kayayyaki masu hadari.
- Bukatar Samar Wa Kotunan Korafe-korafen Zabe Kudaden Gudanarwa
- DPO Ya Kubuta Daga Hannun ‘Yan Bindiga Bayan Shafe Sama Da Watanni 3
Mutanen da su ne dai rundunar tace ta ke zargi da garkuwa da mutane domin biyan kudin fansa, sace-sace a gidajen jama’a, aikata fyade ga mata, da sauran miyagun ayyuka a jihar.
Da yake magana lokacin gabatarwar, CP Sikiru K. Akande, ya ce jami’an rundunar ‘yansanda sun kame mutanen da ta ke zargin ne a karshen mako, ya ce rundunoni jami’an na musamman da su ke aikin dakile miyagun ayyuka su ka yi aikin.
Ya ce “rundunar ‘yansanda a shirye ta ke, ba za mu taba kyale wasu mutanen da ba za su kawo zaman lafiya a jiha ba, duk mai aikata miyagun aiki ba zai kai labari ba” in ji Akande.
Haka kuma kwamishinan ‘yansanda Akande, ya yaba wa gwamnatin jihar da jama’a bisa hadin kai da gudumuwar da suke ba rundunar, ya kuma ba da tabbacin mutanen da aka kamen rundunar za ta gurfanar da su gaban kotu bayan ta kammala bincike.
Da yake magana game da babban zaben 2023 kuwa CP Akande, ya ce rundunar ‘yansanda ta tsara yadda yakin neman zabe zai gudana ba tare da fada ko aikata abin da bai kamata ba, ya kuma ba da tabbacin tsaro da kiyaye lafiyar jama’a lokacin yakin neman zaben.
Kwamishinan ya kuma gargadi daukacin jami’an rundunar ‘yansandanda su tabbatar da tsaro ga jama’a, kada a samu tashin hankali ko aikata abin da bai kamata ba lokacin yakin neman zaben.