Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ‘yan siyasa a wannan kakar zabe da su guji yin amfani da kalaman batanci.
A sakonsa na fatan alheri ga al’ummar Musulmi a wajen Mauludi na murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW), Shugaban ya kuma bukaci ‘yan siyasa da su kaucewa wulakanci da wulakanta abokan hamayya.
- 2023: Matasa A Kano Sun Yi Alkawarin Yi Wa ‘Yan Siyasa Masu Ingiza Su Shaye-shaye Tutsu -Fatima Jikan Dan’uwa
- Kasar Sin Ta Mika Dakin Adana Magunguna Na Zamani Ga Zimbabwe
Shugaban kasar a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya fitar a ranar Juma’a, ya sake yin alkawarin cewa zai tabbatar da sahihin zabe da gaskiya a 2023.
Ya kuma bukaci al’ummar musulmi da su yi koyi da kyawawan dabi’u na Annabi Muhammad (SAW) inda ya ce “mafificiyar hanyar girmamawa shi ita ce koyi da kyawawan halayen Fiyayyen Halitta”.
Buhari ya bayyana cewa “Annabi ya shahara da tawali’u da kuma adalci.”
A cewar shugaba Buhari, “Manzon Allah ya jawo hankalin mutane zuwa ga addinin musulunci ta hanyar gaskiya da rikon amana da adalci da hakuri da juriya”.
Ya bayyana cewa Annabi ya yi rayuwa ta hakuri a karkashin girmama yarjejeniyar wadanda ba musulmi ba domin zaman lafiya.”
Shugaba Buhari ya kara da cewa “Gaskiya na daya daga cikin manya-manyan dabi’un Manzon Allah SAW kuma duk musulmin kirki ya yi koyi da shi.”
Shugaban ya yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga ‘yan Nijeriya da su ba gwamnati hadin kai a kokarin da ake yi na kawar da rashin tsaro da cin hanci da rashawa; su kara girmama mata da yara da masu karamin karfi; da kuma nuna kauna da fahimtar juna.