Gwamnatin tarayya ta fara rabon kayayyakin adana amfanin gona ga manoma a jihohi 19 da ke fadin kasar nan, domin magance barazanar karancin abinci.
Babban sakataren ma’aikatar aikin gona ta kasa, Dakta Ernest Umakhihe ne, ya tabbatar da hakan lokacin da yake kaddamar da rabon kayan ga manoma.
- Yadda Za Ki Gane Yanayin Fatarki
- Sin Ta Yi Kira Da A Taimakawa Gwamnatocin Kasashen Afirka Wajen Inganta Karfinsu Na Amfani Da Albarkatun Halittu
Ya ce bai wa manoman kayayyaki zai ba su damar adana amfanin gonarsu, sakamakon yadda ma fi yawa daga cikin manoma ke asara dalilin rashin kyakkyawan wajen ajiya, tun daga gona zuwa gida.
Umakhihe, ya kuma tabbatar da cewa shirin zai taimaka wajen kawo wadataccen abinci a kasa da kuma farfado da tattalin arziki, inda ya kara da cewa, Gwamnatin tarayya ta gano bakin zaren matsalar killace amfanin gona yadda ya kamata, wanda shi ne dalilin jawo asara mai tarin yawa ga manoma.
Ya ce, ba wa manoma tallafi da kuma samar musu da yanayin da za su kilkace amafanin gonar da suka girbe zai ba su kwarin gwiwa wajen rage asarar da suke tafkawa.