Yau ne, hukumar kula da ‘yancin mallakar fasaha ta kasar Sin ta shirya taron ganawa da manema labarai mai lakabin “Kare ‘yancin mallakar fasaha a cikin shekaru goma da suka gabata”, inda mataimakin shugaban hukumar Hu Wenhui ya bayyana cewa, aikin kare ‘yancin mallakar fasaha ya samu babban sakamako a cikin shekaru goma da suka gabata, tun bayan da aka kira babban taron wakilan JKS karo na 18 a shekarar 2012.
A cikin wadannan shekaru goma, adadin ‘yancin mallakar fasaha na kasar Sin ya karu, kuma ingancinsu ya kyautata. Ya zuwa watan Satumban bana, gaba daya adadin ‘yancin mallakar fasaha da suka samu amincewa a kasar ya kai miliyan 4.081, kuma matsayin kasar Sin a jerin sunayen “Rahoton alkaluman kirkire-kirkire a fadin duniya” da hukumar kare ‘yancin mallakar fasaha ta duniya ta fitar ba da dadewa ba, ya ci gaba daga matsayi na 34 na shekarar 2012 zuwa na 11 a shekarar 2022, wato matsayin kasar Sin ya ci gaba da daguwa a kai a kai a cikin shekaru goma da suka gabata, musamman ma ta fuskar kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha.
Hakazalika, saurin amfani da ‘yancin mallakar fasahar kasar Sin ya karu a cikin shekaru goma da suka gabata, gaba daya adadin lambobin zinariya da aka baiwa bangaren ‘yancin mallakar fasahar kasar ya kai 310, wadanda darajarsu ta kai kudin Sin yuan triliyan 2.5. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)