• English
  • Business News
Tuesday, October 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dalilan Da Suka Sa Kauyukan Sin Samun Ci Gaba

by CMG Hausa
3 years ago
Sin

Wasu abokaina ‘yan Najeriya, wadanda suka taba zama a kasar Sin, su kan ambaci yadda zaman rayuwa a cikin biranen Sin ya burge su, yayin da muke hira. Sai dai na kan tunatar da su cewa, ba abun mamaki ba ne, ganin irin saurin ci gaba da aka samu a kauyukan kasar Sin.

Kauyena yana lardin Anhui dake gabashin kasar Sin, wani wuri ne dake cikin duwatsu. Yayin da nake karami, ba na son komawa kauyen tare da iyayena, saboda hanyar ba ta da kyau: a kan kwashe sa’o’i 10 a cikin jirgin kasa, sa’an nan a ci gaba da hawa tarakta har tsawon awa daya.

  • Ka’idar Sin Daya Tilo A Duniya Ke Tabbatar Da Kwanciyar Hankali A Mashigin Tekun Taiwan

Ban da wannan kuma, bayan gidan da mutanen kauyen suke amfani da shi ba shi tsabta, hakan yana tsorata ni.

Sai dai zuwa yanzu, kauyen ba kamar yadda yake a baya ba. Jirgin kasa mai saurin gudu ya samar da sauki sosai ga mutanen da suke neman komawa kauyen. Kana mutanen wurin sun gina manyan benaye, ga kuma muhalli mai tsabta da kayatarwa. Ban da haka kuma sun fara yin amfani da dakunan dake cikin gidajensu wajen karbar baki masu yawon shakatawa.

To, me ya sa ake samun ci gaba sosai a kauyukan kasar Sin, cikin gomman shekaru da suka wuce?
Dalili na farko, a ganina, shi ne niyyar gwamnati ta raya kayuka, da yadda take kokarin aiwatar da niyyar.

LABARAI MASU NASABA

Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Ghana Da Firaministar Mozambique

Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Sun Jinjinawa Rawar Da Mata Ke Takawa A Harkokin Ci Gaba

Babbar manufar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin dake kan karagar mulki a kasar, ita ce kokarin kyautata zaman rayuwar jama’a. Saboda haka gwamnatin kasar ba za ta taba barin ragowar sassan kasar, ko kuma wasu mutane a baya ba, yayin da take kokarin raya tattalin arzikin kasar.

Hakan ya sa gwamnati ta fito da dimbin manufofi wajen raya kauyuka, da kyautata zaman rayuwar manoma. Misali taimakawa kauyuka wajen janyo jari, da samarwa manoma fasahohin zamani na aikin gona, da samar da rance don raya aikin yawon shakatawa a yankin karkara, da dai sauransu.

Dalili na biyu, shi ne yadda wasu matasan kauyuka suka komawa gida, bayan da suka samu ilimi, don taimakawa wajen raya kauyukansu.

A cikin kauyukan da na ziyarta a shekarun baya, na kan ga wasu matasan da suka kammala karatun jami’a a cikin manyan birane, inda suka shafe wasu shekaru suna aiki a can, daga bisani sun koma kauyukansu, sun fara aiki a matsayin jami’ai. Yadda aka wayar musu da kai, ya samar musu da damammakin raya wasu sana’o’i da suka dace da yanayin kauyukan, kana sun fahimci muhimmancin yin amfani da manufofin da gwamnati ta tsara na raya yankunan karkara.

Ban da wannan kuma, dalili na uku shi ne al’adun Sinawa na jure wahalhalu da kokarin aiki.

A kauyukan da na je, na ga wasu tsoffi da yawa da suke gudanar da ayyuka daban daban, misali sayar da kaya, ko kuma nuna fasahohin hannu, har ma wasunsu na tuka manyan motocin tsabtace muhalli. Haka ma dattawa na kokarin aiki, balle ma matasa.

Sinawa suna daukar kokarin aiki a matsayin wata muhimmiyar da’a. Kana nagartattun manufofin gwamnati su ma sun sa mutanen kasar ke da wani tunani na kokarin aiki da samar da hidimomi, don kyautata rayuwarsu, gami da ba da gudunmowa ga ci gaban kasa.

A cikin kauyukan kasar Sin, ana iya ganin yadda mazauna suke da imanin cewar, za su kara jin dadin zaman rayuwarsu a nan gaba. Wannan imani ya tabbatar da cewa, ba za a taba daina kokarin raya kauyukan kasar, da kyautata zaman rayuwar jama’ar wuraren ba. (Bello Wang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Ghana Da Firaministar Mozambique
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Ghana Da Firaministar Mozambique

October 14, 2025
Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Sun Jinjinawa Rawar Da Mata Ke Takawa A Harkokin Ci Gaba
Daga Birnin Sin

Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Sun Jinjinawa Rawar Da Mata Ke Takawa A Harkokin Ci Gaba

October 13, 2025
Matakan Da Sin Ta Dauka Na Mai Da Martani Ga Bincike Mai Lamba “301” Da Amurka Ta Gudanar Sun Zama Wajibi Don Kare Hakkinta
Daga Birnin Sin

Matakan Da Sin Ta Dauka Na Mai Da Martani Ga Bincike Mai Lamba “301” Da Amurka Ta Gudanar Sun Zama Wajibi Don Kare Hakkinta

October 13, 2025
Next Post
Li Song: Tunanin Cacar Baka Barazana Ne Ga Daidaiton Duniya

Li Song: Tunanin Cacar Baka Barazana Ne Ga Daidaiton Duniya

LABARAI MASU NASABA

Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Ghana Da Firaministar Mozambique

Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Ghana Da Firaministar Mozambique

October 14, 2025
‘Yan Majalisa 60 Sun Yi Barazanar Ficewa Daga PDP

PDP Ta Ɗage Babban Taronta Biyo Bayan Ficewar Wasu Manyan Jiga-jigai

October 14, 2025
An Kashe Mutum 3, Wasu 7 Sun Jikkata Sakamakon Ɓarkewar Rikici A Jihar Jigawa

An Kashe Mutum 3, Wasu 7 Sun Jikkata Sakamakon Ɓarkewar Rikici A Jihar Jigawa

October 14, 2025
Rashin Tsaro A Nijeriya Ba Zai Ƙare Ba Matuƙar Ba A Samar da Ayyukan Yi Da Mulki Na Adalci Ba – Amaechi

Rashin Tsaro A Nijeriya Ba Zai Ƙare Ba Matuƙar Ba A Samar da Ayyukan Yi Da Mulki Na Adalci Ba – Amaechi

October 14, 2025
Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa

Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa

October 14, 2025
‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Jarida A Kan Hanyarsa Ta Zuwa Ɗaukar Horo A Kwara

‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Jarida A Kan Hanyarsa Ta Zuwa Ɗaukar Horo A Kwara

October 14, 2025
Zaman Gidan Yari Ya Nuna Min Mutanen Da Ya Kamata Na Yi Hulɗar Siyasa Da Su — Faruk Lawan

Zaman Gidan Yari Ya Nuna Min Mutanen Da Ya Kamata Na Yi Hulɗar Siyasa Da Su — Faruk Lawan

October 14, 2025
Majalisa Na Shirin Sauya Lokacin Zaɓen 2027 Zuwa Nuwamba 2026

Majalisa Na Shirin Sauya Lokacin Zaɓen 2027 Zuwa Nuwamba 2026

October 13, 2025
Yajin Aiki: Malaman Jami’a Sun Ce Barazanar ‘Ba Aiki, Ba Biya’ Ba Zata Tsorata Su Ba

Yajin Aiki: Malaman Jami’a Sun Ce Barazanar ‘Ba Aiki, Ba Biya’ Ba Zata Tsorata Su Ba

October 13, 2025
Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Sun Jinjinawa Rawar Da Mata Ke Takawa A Harkokin Ci Gaba

Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Sun Jinjinawa Rawar Da Mata Ke Takawa A Harkokin Ci Gaba

October 13, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.