Wasu daruruwan ‘yan Nijeriya sun gudanar da zanga-zangar lumana a Abuja a kan yadda wasu ‘yan kasar waje, musamman ‘yan kasar China ke yanka Jakuna ta haramtacciyar hanya, wanda hakan ya haifar da wahalar Jakunan.
Zanga-zangar ta zo a kan gaba, ganin cewa Sanatoci na tafka muhawara a kan sa ido kan kasuwancin Jakuna a kasar.
- 2023: Kuri’a Miliyan 95 Ce Za Ta Bayyana Wanda Zai Gaji Buhari – INEC
- Kamfanin Simintin Dangote Ya Raba Wa Abokan Kasuwancinsa Kyaututtuka Na Miliyan 21
Sai dai, an samu rabuwar kawunan a kan tattuanawar a tsakanin masu ruwa da tsaki a fannin dillalai da sanarwar sayar da Jakunan ciki har da wasu ‘yan majalisar.
Wasu sun bukaci a soke yanka Janunan, inda wasu kuma suke ce, sa ido a kan hada-hadar da kasuwancinsu zai rage yawan yadda ake fasa kaurinsu zuwa ketare, inda kuma kara kiwata wasu Jakunan, zai taimaka kara yawansu a kasar.
Masu zanga-zangar sun ce, ana ci gaba da yanka Jakunan duk da cewa, Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin hanawa.
Kungiyoyin kare rajin hakkin dabobbi ne suka gudanar da zanga-zangar, inda wadanda suka jagoranci zanga-zangar, Barista Emmanuel Onwudiwe da Ogwuche Emmanuel suka yi kira ga mahukunta a kasar nan da su dauki matakan suka dace, domin a dakatar da yanka Jakunan da kuma wahalar da su.
A ckin sanarwar da suka fitar a gun zanga-zangar sun yi nuni da cewa, hada-hadar kasuwancinsu da ake yi, a kasar nan, zai samar aa Nijeriya kudade har yawansu ya kai Naira biliyan 60, inda kuma hakan zai iya samarwa da ‘yan Nijeriya sama da 250,000 ayyukan yi.