Abokai, ko akwai wahalar samun jiyya a wuraren dake da nisa daga birane a wurin ku? Tun bayan kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin, kullum gwamnatin kasar na kokarin daidaita wannan matsala. Yau ma “Duniya a zanen MINA” na bayyana muku tsarin gwamnatin Sin na ba da jiyya ga dukkanin kauyuka.
Saurayin dake cikin zanen sunansa Marghulam Abdukrem, ya karanta ilmin likitanci a kyauta bisa tallafin gwamnati a fannin ilmin likitanci a watan Yuli, kuma bayan da ya kammala karatun, an tura shi zuwa kauyen Kokbash dake garin Baishtugman, na birnin Aksu dake jihar Xinjiang, a matsayin likitan wurin.
A wasu wuraren dake da nisa da birane kamar wannan kauye, an fuskanci matsalar karancin likitoci da magunguna a baya, abin da ya sa al’ummar wurin da dama sun kasa samun damar samun jiyya.
Domin warware irin wannan matsala, gwamnatin kasar Sin na daukar wasu matakai masu dacewa, ciki hadda rarraba albakatun ba da jiyya yadda ya kamata da daga matsayin ba da jiyya a wurare daban-daban, da kyautata hukumomin ba da jiyya da habaka masu aikin jiyya a wuraren da dai sauransu, ta yadda za a tabbatar da cewa, ana samar da jiyya ba tare da matsala ba.
Shirin horar da likitocin da za a tura su kauyuka kyauta, daya ne daga cikin wadannan matakai, kuma ya zuwa yanzu, ana horar da dalibai fiye da dubu 70 a wannan fanni, kuma daga cikinsu dalibai kimanin dubu 35 sun kammala karatunsu, an kuma tura su kauyuka daban-daban don su zama likitoci.
A bana a jihar Xinjiang, matasa 229 kamar Marghulam Abdukrem da suka samu ilmin likitanci kyauta karkashin shirin gwamnati, sun tafi kauyuka daban-daban na jihar.
Wadannan matasa sun ci gajiyar wannan shirin gwamnati sosai. Ba ma kawai sun samun aikin yi karkashin wannan shiri ba, har ma sun taka rawarsu wajen daga karfin ba da jiyya a kauyuka.
Ya zuwa karshen shekarar 2021, kasar Sin ta kafa hukumomin jiyya a da suka game dukkan kauyukan kasar.
Manoman kasar Sin suna iya samun jiyya a cikin kauyensu, matakin da ya kyautata zaman rayuwarsu. (Mai zane kuma mai rubuta: MINA)