Sabon rikici ya barke a cikin jam’iyyar APC ta Jihar Nasarawa sakamakon dakatar da shugaban matasa, Alhaji Abdullahi Masu.
A ranar Lahadin da ta gabata ce, mambobin jam’iyar APC a matakin gunduna na Ciroma da ke karamar hukumar Lafiya suka bayar da sanarwan dakatar shugaban matasan jam’iyar na jihar, Alhaji Abdullahi Masi saboda samun sa da rashin da’a.
Shugaban gunduma na jami’ar, Mohammed Suleiman Ramalan shi ne ya sanar da hakan a taron manema labarai da suka kira a lafiya fadar gwamnatin Jihar Nasarawa.
Mohammad ya ce wannan ummurnin da amincewar mambobin Jam’iyyar APC kowa ya sa hannun. Ya ce gunduman Ciroma tanada kuri’u mai yawa wanda zai bai wa gwamnan jihar daman samun nasara, saboda haka bai kamata a ce daga wannan gundumar za a fara samun matsala a tafiyan APC ba.
Shugaban APC ta gunduman Ciroman ya kara da cewa za su bincika laifufukan da ake zargin shugaban matasan da aikatawa idan har hakan ya tabbata za su dauki mataki na gaba.
Sai dai shugaban matasan APC, Alhaji Abdullahi Masi ya ce wannan dakatarwan da aka ce an yi masa bai samu takardan ba, kuma ba su yi shi a ka’ida ba.
Ya ce, hakan baya rasa nasaba da makircin wasu mutane da ba su bukatan ci gaban jam’iyyar APC da nasaran Gwamnan Abdullahi Sule.