Gwamna Jihar Bauchi, Bala Muhammad ya bayyana cewa salon mulkin takwaransa na Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya zama abin alfahari ga illahirin al’ummar shiyyar Arewa Maso Gabas da ma kasa baki daya.
Gwamna Bala wadda ke maida jawabi a lokacin da Gwamna Babagana Umara Zulum ya kawo masa ziyarar ta’aziyyar rasuwar yayansa, Abubakar Muhammad Duguri da ya rasu a kwanakin baya yana da shekara 69 a duniya.
Gwamnan ya ce: “Tabbas ka nuna kwazo da kokari a jagorancinka. Irin salon mulkin da kake gudanarwa a Borno. Muna kokarin koyi daga gare ka. Suna kirana Kauran Bauchi, amma ina tunanin kai kuma Kauran Arewa Maso Gabas ne.
“Duk da fama da aka yi da ‘yan ta’adda amma ka yi tsayuwar daka wajen dakile su, wanda hatta Shugaban kasa na alfahari da kai”.
Ya kuma ce nasarar da gwaman na Borno ya samu kan ‘yan ta’addan Boko Haram abun jinjina da alfahari ne bisa yadda ya yi kokari wajen ganin ya kare jihar da ma shiyyar Arewa Maso Gabas hadi da kasa baki daya.
Tun da farko Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce ya zo jihar ne domin mika ta’aziyya bisa rasuwar dan’uwan Gwamna Bala, ya yi addu’ar Allah jikansa ya gafarta masa.