A kwanakin baya ne, mahaukaciyar guguwar Juliet ta afkawa kasashe da dama dake yankin tsakiya da kudancin Amurka. Kasar Sin ta kira tauraron dan-Adam da ake sarrafawa daga nesa a karon farko, don samar da tallafin fasahar sararin samaniya, a kokarin yaki da ambaliyar ruwa da rage radadin bala’i.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Mao Ning ta bayyana a yayin da take karin haske game da tambayoyin da aka yi mata kan wannan batu Jumma’ar nan cewa, ci gaban kimiya da fasaha da kasar Sin ta samu, zai kasance a bude tare da damawa da kowa, da cin moriyar juna da yin musaya, kuma ba jama’arta kadai ne za su ci gajiyar hakan ba, har ma da al’ummar duniya baki daya. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)