An bude babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin JKS karo na 20, da misalin karfe 10 na safiyar yau Lahadi a Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Wakilan jam’iyyar, gami da wadanda aka ba su goron gayyata na musamman sama da 2300 sun halarci taron, tare da wasu da ba ’yan jam’iyyar kwaminis din ba da sauransu. Za kuma a rufe taron a ranar 22 ga wata.
A wajen taron, za’a saurara, gami da duba rahoton aiki na kwamitin kolin JKS na 19, da duba rahoton aikin da kwamitin ladabtarwa na kwamitin koli na JKS na 19 ya gabatar. Kana, za’a amince da gyararren shiri na kundin ka’idojin jam’iyyar JKS, da kuma zabar membobin kwamitin kolin jam’iyyar da na kwamitin ladabtarwar jam’iyyar a sabon zagaye.
Jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin mai tarihin shekaru 101, ta shafe tsawon shekaru 73 tana kan karagar mulkin kasar Sin, wato tun kafuwar Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin.
Babban taron wakilan jam’iyyar, gami da kwamitin kolinta, su ne hukumar koli ta jam’iyyar. A kan gudanar da babban taron wakilan jam’iyyar a duk bayan shekaru biyar.
A wajen taron, shugaba Xi Jinping ya gabatar da muhimmin rahoto, a madadin kwamitin kolin jam’iyyar na 19.
Xi ya ce, a shekaru 10 da suka gabata, yawan GDPn kasar Sin ya karu daga kudin Sin Yuan tiriliyan 54, har zuwa tiriliyan 114, kana jimillar tattalin arzikin kasar Sin ta dauki kaso 18.5 bisa dari, na jimillar tattalin arzikin duk duniya, adadin da ya karu da kaso 7.2 bisa dari, wanda ya sa kasar ta zama ta biyu a duniya.
Shugaba Xi ya kuma ce, kasar Sin ta zama babbar aminiyar cinikayya ga kasashe da yankuna sama da 140, kuma jimillar kudin cinikayyar kayayyaki ta kasar tana kan gaba a duniya, kana, yawan jarin waje da kasar Sin ta jawo, da yawan jarin da ta zuba a sauran kasashe duk suna kan gaba.
A halin yanzu kasar Sin tana habaka bude kofarta ga kasashen waje a fannoni daban-daban.
Xi ya kara da cewa, kasar Sin ta samu babban ci gaba wajen raya wasu muhimman fasahohi, da kara bunkasa sabbin sana’o’i da dama, ciki har da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da dan Adam a sararin samaniya, da binciken duniyar wata da duniyar Mars, da binciken yankin ruwan teku mai zurfi, da nazarin manyan na’urori masu kwakwalwa, da taurarin dan Adam, da amfani da makamashin nukiliya don samar da wutar lantarki, da kera manyan jiragen sama, da harhada magunguna da sauransu, al’amarin da ya sa Sin ta shiga jerin kasashen dake kan gaba a duniya, wajen yin kirkire-kirkire.
Har wa yau, shugaba Xi ya nuna cewa, ya dace kasar Sin ta raya ingantaccen tsarin tattalin arziki irin na kasuwa mai salon gurguzu, da tsayawa gami da kyautata babban tsarin tattalin arziki irin na gurguzu, da kara habaka tattalin arziki irin na gwamnati, da kuma karfafa gwiwa da jagorantar ayyukan raya tattalin arzikin da ba na gwamnati ba, ta yadda kasuwannin kasar za su kara taka muhimmiyar rawa wajen daidaita albarkatu, kuma gwamnatin kasar ita ma za ta kara taka rawarta.
Xi ya jaddada cewa, ya dace a raya tsarin sana’o’i irin na zamani, da maida hankali sosai kan raya sassan da suka shafi hada-hadar kudade kai-tsaye, da raya sabbin masana’antu, da gaggauta gina kasar Sin mai karfin yin kere-kere, mai karfin binciken sararin samaniya, mai karfin zirga-zirgar ababen hawa, mai karfin amfani da yanar gizo ta intanet, mai karfin fasahar sadarwar zamani da sauransu.
Har wa yau, ya kamata a nuna azama wajen farfado da yankunan karkara daga dukkan fannoni, da nuna fifiko wajen samar da ci gaban ayyukan noma da yankunan karkara, da kara saurin raya kasar Sin mai karfin aikin noma.
Shugaba Xi ya kara da cewa, ana bukatar a ci gaba da habaka bude kofar kasar Sin ga kasashen ketare, da gagguta raya kasar mai karfin harkokin kasuwanci, da taimakawa ci gaban aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”, a wani kokari na kiyaye tsarin tattalin arzikin duniya, da huldar tattalin arziki, da kasuwanci dake kunshe da bangarori daban-daban. (Murtala Zhang)