Gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Duoye Diri, ya ayyana hutun kwanaki bakwai ga ma’aikatan gwamnati sakamakon matsalolin da ake fuskanta sakamakon iftila’in ambaliyar ruwa da ya addabi jihar.
A wani jawabi da ya yi a fadin jihar a safiyar ranar Talata, Gwamna Diri ya ce ambaliyar annoba ce da ta addabi sauran jihohin kasar nan da dama.
- Sojoji Sun Cafke Mutum 40 Masu Yi Wa ‘Yan Ta’adda Safarar Kayan Abinci
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Hakimi, Sun Yi Awon Gaba Da ‘Ya’Yansa 5 A Filato
Ya bayyana cewa kusan mutane miliyan daya a cikin al’ummomi, inda sama da mutane 300 a jihar suka rasa matsugunansu yayin da aka samu rahoton mutuwar wasu.
A cewar gwamnan jihar na fuskantar matsalar jin kai inda sama da mutane miliyan daya suka rasa matsugunansu a fadin kananan hukumomin Sagbama, Ekeremor, Kudancin Ijaw, Ogbia, Yenagoa, Nembe da Kolokuma Opokuma a yayin da ‘yan kasuwa suka rufe, aka yi asarar dukiyoyi tare da lalacewar gonaki.
“A nan ina ba da umarni ga dukkan ma’aikatan gwamnati ban da wadanda ke kan muhimman ayyuka da a ba su lokaci daga aiki na mako guda,” in ji gwamnan.
“Bari in yi kira na musamman ga dillalai, musamman na man fetur, abinci, ruwa da magunguna da kada su yi amfani da lamarin. Dole ne mu zama masu kiyaye ’yan’uwanmu.
“Gwamnati ta kuma lura cewa a irin wannan lokacin na wahala, wasu bata-gari suna cin gajiyar jama’a wajen aikata laifuka. Bari in bayyana a fili cewa za mu lamunci aikata laifuka b.”
Ya ce muhimman ababen more rayuwa kamar asibitoci da tituna da gadoji da makarantu da suka hada da jami’ar Neja Delta ta Amassoma mallakin gwamnati, asibitin koyarwa na Jami’ar Neja Delta, Okolobiri, da Jami’ar Afrika, Toru-Orua, abin ya shafa sosai.
Diri ya kara da cewa, idan ba a kai wa jihar dauki ba, akwai yiwuwar sake yin asarar dukiya, inda ya bukaci a kai wa jihar dauki.