Mataimakin ministan ma’aikatar kula da harkokin kare muhalli ta kasar Sin Zhai Qing, ya ce a matsayin Sin na kasa mai tasowa mafi girma a duniya, za ta gudanar da babban aikin rage fitar da iskar Carbon mai dumama yanayi, kaza lika kasar Sin za ta dauki mafi kankantar lokaci a tarihi, daga kololuwar matakin fitar da iskar Carbon, zuwa mafi karancin matakin fitar da shi.
Zhai wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar yau Juma’a, a gefen babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (JKS) na 20, ya kara da cewa, Sin tana taka rawar da ta dace a fannin shawo kan sauyin yanayi, karkashin hadin gwiwar kasashe masu tasowa. Har ila yau ta yi iya yin ta, wajen taimakawa wasu kasashe masu tasowa, musamman kananan tsibirai, da kasashen Afirka, da kasashe masu karancin ci gaba, ta yadda za su inganta matakan rage mummunan tasirin sauyin yanayi.
Jami’in ya kara da cewa, a nan gaba, kasar Sin za ta yi aiki tukuru tare da dukkanin sassa, domin jagorantar ayyukan daidaita sauyin yanayi, da kara zurfafa hadin gwiwar kasashe masu tasowa a fannin, kana za ta ba da karin gudummawarta, a fannin shawo kan kalubalen sauyin yanayi a matakin kasa da kasa. (Saminu Alhassan)