Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya sha alwashin ci gaba da yakar da cin hanci da rashawa kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.
Tinubu ya yi alkawarin ci gaba da sauye-sauyen da Buhari ya yi na ma’aikatan gwamnati don rage cin hanci da rashawa.
- Sin Ta Yi Rawar Gani Wajen Tallafawa Ayyukan Daidaita Sauyin Yanayi
- ‘Yan Wasan Real Madri 10 Ne Suka Taba Lashe Ballon d’Or
Ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da yake bayyana diraftin manufofin yakin neman zabensa a Abuja.
Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da rage barna a ma’aikatan gwamnati idan ya gaji Buhari a 2023.
“Za mu ci gaba da aikin gwamnati mai ci na sake fasalin ma’aikatan gwamnati don yaki da cin hanci da rashawa, daidaita hukumomi da rage almubazzaranci,” in ji takarara.
Sai dai an caccaki Tinubu kan cin hanci da rashawa da kuma tara dukiyar da ba a san hallacinta ba.
Sau tari dai tsohon gwamnan na Legas ya ki amsa tambayoyi kan mallakar wani kamfani mai zaman kansa Alpha Beta da ke karbar haraji a madadin Jihar Legas.
Ana kyautata zaton yana da babban hannun jari a kamfanin, wanda ya dauki nauyin kula da harajin Jihar Legas a karkashinsa lokacin da yake gwamnan Jihar Legas.