Hukumar bada agajin gaggawa (NEMA), ta sake karbar wasu ‘yan Nijeriya 137 da suka makale a kasar Libya.
Hukumar NEMA ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata a Legas.
- Kotu Ta Bada Umarnin Kwace Wasu Kadarorin Diezani Alison-Madueke A Abuja
- Da Dumi-Dumi: WhatsApp Ya Dawo Aiki A Nijeriya Da Wasu Sauran Kasashen Duniya
Hukumar ta ce mutanen da suka dawo sun isa filin jirgin saman Murtala Muhammad, da ke Ikeja, a cikin jirgin Al Buraq Air Boeing 737-800 da misalin karfe 5:15 na yammacin ranar Litinin.
NEMA ta ce wadanda aka dawo da su sun hada da maza 80, mata 52 da jarirai uku.
Mista Mustapha Ahmed, Darakta-Janar na NEMA, wanda ya karbi mutanen da suka dawo a hukumance a madadin gwamnatin tarayya, ya shawarce su da su yi koyi da abubuwan da suka faru kuma su kasance masu bin doka da oda.
Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), ya bayar da rahoton cewa, an kwaso kusan ‘yan Nijeriya 3,000 daga kasar Libya tun daga watan Janairu.
Har ila yau, rahoton ya ce a ranar Lahadi, NEMA ta karbi ‘yan Nijeriya 542 da suka makale a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).