Shugaban kasa Muhammadu ya shawarci jami’an tsaron kasar da daukacin al’ummar kasar da su ci gaba da yin taka-tsantsan da harkokin tsaro, kuma ya bukaci kowa ya kwantar da hankalinsa.
Ya bukaci ‘yan kasar da su kwantar da hankalinsu, inda ya ce akwai sauye-sauye da aka samu kan sha’anin tsaro.
- Ta Yaya Za A Kubutar Da Kananan Yaran Amurka Daga Harbe-harben Bindiga
- Malaman Jami’o’i Sun Koma Bakin Aiki Cikin Yunwa – Shugaban ASUU
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar, shugaban kasar ya ce Nijeriya ba ta bar baya da kura ba a cikin jerin barazanar ta’addanci a cikin shawarwarin da ofishin jakadancin Amurka ya bayar.
Ya ce shawarwarin tafiye-tafiye na Birtaniya da Amurka sun kuma lura da yiwuwar kai hare-haren ta’addanci a yawancin kasashen yammacin Turai.
Hakika, Buhari ya ce shawarar Birtaniya da Amurka ga ‘yan kasarsu na yin balaguro zuwa kasashensu na dauke da wannan gargadin.
Abin takaici, ta’addanci gaskiya ne a duniya. Sai dai ya ce hakan ba yana nufin za a kai hari Abuja ba.
“Tun daga harin da aka kai gidan yarin Kuje a watan Yuli, an karfafa matakan tsaro a babban birnin tarayya Abuja da kewaye.
Akwai sa ido da katse hanyoyin sadarwar ‘yan ta’adda don tabbatar da dakile kowace irin barazana.
“Ana dakile hare-hare. Jami’an tsaro suna aiki don kawar da barazana da kiyaye lafiyar ‘yan kasa – yawancin ayyukansu ba a gani saboda kusan a boye suke.
“Tsaron ‘yan Nijeriya shi ne babban fifikon gwamnati. Jami’an tsaro suna aiki ba dare ba rana don kiyaye kowace irin barna,” in ji shi.
Shugaban ya ba da tabbacin cewa gwamnati na kan gaba a harkar tsaro a kasar.
Ya kuma kara da cewa, ‘yansanda da sauran hukumomin tsaro suna kokari wajen tunkarar lamarin, kamar yadda ya tabbata daga yadda akasarin abokan huldar Nineriya, ciki har da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya.
Shugaba Buhari ya ya bai wa sojoji da sauran jami’an tsaro kan yadda aka samu sauyin kan harkar tsaron kasar nan, ya kuma ba da umarnin a kara daukar matakan rigakafi kuma kada a yi kasa a gwiwa a lokacin bukukuwan da ke tafe.
Shugaba Buhari ya bayyana kwarin gwiwarsa na ganin yadda sojoji da sauran jami’an tsaro da na leken asiri ke yi tare da goyon bayan fararen hula, ya ce al’ummar kasar za su yi nasara a kan kalubalen da suke fuskanta a halin yanzu.