Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu matafiya hudu a hanyar Ekiti zuwa Oke Ako a karamar hukumar Ajoni (LCDA) a Jihar Ekiti.
An ce matafiyan na komawa Ibadan, babban birnin Oyo, bayan sun halarci wani taro a Jihar Kogi.
- Yekuwar Kai Hare-Hare Abuja: British Airways Ya Dawo Da Jigilar Fasinja Zuwa Abuja
- An Dakatar Da Mu Don Mun Nemi Mukamin Alkalin Babbar Kotun Kebbi – Wasu Alkalai
Wata majiya ta shaida wa NAN cewa an sace matafiya ne a ranar Lahadi.
“Mutane hudun da aka sace suna dawowa ne daga wani taron da aka yi a Kogi zuwa Ibadan a kan hanyar Irele Ekiti da Oke Ako,” kamar yadda majiyar NAN ta ruwaito.
“Ba mu ji komai daga bakin ‘yan bindigar ba tun jiya kuma muna fatan za su tuntubi iyalansu, watakila don neman kudin fansa.”
A cewar NAN, Kehinde Abejide, shugaban al’ummar Irele-Ekiti, ya yi Allah-wadai da lamarin, ya kuma bukaci Biodun Oyebanji, gwamnan Ekiti da ya dauki matakan inganta tsaro a cikin al’umma.
“Wadannan mutane hudu suna komawa Ibadan ne lokacin da aka kai musu hari aka yi garkuwa da su da safiyar Lahadi, kuma ba mu ji komai ba tun lokacin da aka kwashe su zuwa,” in ji Abejide.
“Muna kuka muna rokon gwamnati ta taimaka mana a wannan yanki, amma ga dukkan alamu babu abin da ke faruwa, musamman idan aka yi la’akari da abubuwan da ke faruwa a cikin al’umma.
“Ko da yake a baya mun yi shirye-shirye m a nan dangane da tsaro, amma a banza.
“Bari in yi kira ga gwamnan Ekiti da ya yi wani abu cikin gaggawa kan rashin tsaro kafin a halaka mutanenmu da daukacin al’ummar Ajoni LCDA.
“Akwai bukatar samar da wasu jami’an soja a tsakanin Irele da Oke Ako, wanda za su taimaka wajen dakile duk wani harin da ‘yan bindigar za su iya kai musu, domin da alama suna cin gajiyar rashin tsarin tsaro a nan.”
Sunday Abutu, kakakin ‘yansandan Ekiti, ya ce zai yi tsokaci kan lamarin idan ya samu karin bayani.