Shugaban sashen Hukumar zana Jarrabawar kammala makarantun sakandare ta nahiyar Afirka (WAEC), Patrick Areghan ya bayyana cewa, hukumar ta kama ma’aikatanta na wucin-gadi masu sa Ido lokacin gudanar da jarrabawar bisa zarginsu da hannu wajen aikata magudin Jarrabawar ta WAEC.Â
Areghan ya sanar da hakan ne a lokacin da yake zagayen daliban da ke zana Jarrabawar a wasu cibiyoyi hudu da ke garin Abuja.
“An kama ma’aikatan ne, a jihohin Legas da Kano da Beyelsa da Kaduna.
“Labari mai kyau shi ne, mun kama su kuma tabbas za su fuskanci Hukunci, inda ya kara da cewa, masu sa Idon sune babban kalubalen mu. Abin takaicin irin wadannan masu sa Idon, an turo su ne daga ma’aikatar ilimi ta jihohi domin suyi aikin sa Ido da kula da Dalibai.”
Areghan Ya sanar da cewa, hukumar ta na tsare dasu a wurin Jami’an ‘yan sanda kuma ba da jimawa ba za a mika su gaban kuliya domin yanke musu hukunci.